Amarya Ta Cinnawa Gidan Mijinta Wuta Kan Abu 1 a Adamawa

Amarya Ta Cinnawa Gidan Mijinta Wuta Kan Abu 1 a Adamawa

  • Wata amarya mai suna Amina Hassan ta shiga hannun ƴan sanda a jihar Adamawa bisa zargin cinnawa gidan mijinta wuta
  • Amina Hassan mai shekara 20 a duniya ta ɗauki wannan matakin ne bayan mijinta ya ƙi yarda ya sake ta
  • Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cafke Amina inda ta ce tana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - An cafke wata amarya ƴar shekara 20 mai suna Amina Hassan daga karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa, da laifin cinnawa gidan mijinta wuta.

An ce Amina ta dauki matakin ne saboda mijinta ya ƙi yarda ya datse igiyar auren da ke tsakaninsu, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Magidanci ya bindige abokinsa a Adamawa, ƴan sanda sun ɗauki mataki

Amarya ta cinnawa gidan mijinta wuta
Amarya ta kona gidan mijinta a Adamawa Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An ce ma'auratan biyu dai sun ƙulla yarjejeniya kafin aurensu cewa mijin zai sake ta bayan an ɗaura musu aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa, Amina ta sanar da iyayenta cewa ba ta da sha’awar auren kwanaki kaɗan kafin a ɗaura musu aure.

Duk da haka, sun dage cewa dole ne a yi bikin saboda sun riga sun raba katunan gayyata, rahoton Peace FM ya tabbatar.

Bayan an ɗaura auren ne ta nemi taimakon wani boka don ya sa mijinta ya tsane ta ya sake ta. Bokan ya bayyana cewa ya yi sihiri kuma ya karɓi Naira 12,000 a matsayin ladan aikin da ya yi mata.

Sai dai, sihirin da bokan ya yi sai ya sanya Amina ta tsani mijinta a maimakon shi ya tsane ta.

Me ƴan sanda suke yi a kan lamarin?

Kara karanta wannan

To Fa: Ana jajibirin zaɓe, Ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar APC ya sha da ƙyar, bayanai sun fito

Bayan da rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke ta, wacce ake zargin ta amsa laifin ta.

A yanzu haka ana kan binciken lamarin kamar yadda kwamishinan ƴan sandan jihar, Afolabi Babatola ya bayar da umarni.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ambato Amina a ranar Talata tana cewa:

“Mun ƙulla yarjejeniya cewa zai sake ni bayan auren. Na roƙe shi ya sake ni, amma ya ƙi yarda."

Ango Ya Halaka Amaryarsa Kan Abinci

A wani labarin kuma, wani matashin magidanci mai suna Salami Anedu mai shekara 21 a duniya, ya halaka matarsa Esther Friday, har lahira kan rigimar abinci a jihar Edo.

Rahotanni sun yi nuni da cewa wanda ake zargin ya yi amfani da itace wajen salwantar da ran matarsa har lahira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel