Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Motar Ɗalibai Wuta, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

Innalillahi: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Motar Ɗalibai Wuta, Sun Tafka Mummunar Ɓarna

  • Wasu mutane ɗauke da bindigu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan motar ɗaliban makaranta a jihar Enugu
  • An tattaro cewa maharan sun kashe ɗaliba mace ɗaya yayin da wasu da dama su ke kwance rai hannun Allah a Asibiti
  • Shugaban makarantar ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai harin ne bayan sun tashi daga makaranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga da ake zaton Fulani ne sun farmaki motar ƴan makaranta mallakin kwalejin St Paul da ke Eke, ƙaramar hukumar Udi a jihar Enugu.

Yan bindiga sun farmaki motar ɗalibai a jihar Enugu.
Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Motar Dalibai Wuta a Jihar Enugu, Sun Kashe Daya Hoto: thenation

Ƴan bindigan, waɗanda ake zargin su ke yawan yin garkuwa da mutane a yankin, sun kashe ɗaliba ɗaya mace yayin da wasu da dama suka ji raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Mutane sun mutu yayin da Fulani suka yi arangama da 'yan banga a kasuwar Jihar Neja

Jaridar The Nation ta samu labarin cewa da yawa daga cikin wadanda suka samu raunukan harbin bindiga a halin yanzu suna kwance rai hannun Allah a wani asibiti da ba a bayyana ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda maharan suka farmaki Motar Bas ta ɗalibai

An tattaro cewa yan bindigan sun bude wa motar Bas din ɗaliban wuta da nufin tilasta wa diraban ya tsaya, amma diraban ya yi ta maza ya ƙi tsayawa.

A wani faifan bidiyo da ke yawo, an ga gawar ɗalibar da maharan suka kashe da kuma sauran ɗaliban da suka tsira daga harin.

Wata murya a bidiyon ta bayyana cewa:

"Makiyaya sun kai wa dalibanmu hari a hanyar komawa gida bayan tashi daga makaranta, an harbe daya daga cikinsu har lahira, wasu hudu kuma sun ji raunin harbi."
“Duba gawar karamar dalibar da suka kashe, wannan na cikin mawuyacin hali, (ya nuna wata da ke kwance) muna addu'ar Allah ya sa ta rayu, sau huɗu suka harbe ta."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun Buɗe wa mazauna garuruwa biyu wuta, sun kashe mutane da yawa

Shugaban makarantar, Rebaran Fada Frank a wata hira ta wayar tarho da manema labarai, ya tabbatar da harin, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

"Eh da gaske ne, mun tashi makaranta da misalin ƙarfe 3:30 jiya, a hanyar komawa gida ne aka kai wa ɗaliban hari, da yawa sun samu raunuka, daga baya ɗaya ta mutu," in ji shi.

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ci tura.

Yan banga da Fulani sun yi artabu a Neja

A wani rahoton kuma Mutum biyu sun mutu yayin da ƴan banga da Fulani suka yi arangama a kasuwar Beji, ƙaramar hukumar Bosso a jihar Neja.

Rahoto ya nuna cewa mutum bakwai na kwance a Asibitin Beji ana kula da lafiyarsu bayan samun rauni a faɗan da ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel