'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Buɗe Wa Mazauna Garuruwa Biyu Wuta, Sun Kashe Mutane da Yawa

'Yan Bindiga Sama da 100 Sun Buɗe Wa Mazauna Garuruwa Biyu Wuta, Sun Kashe Mutane da Yawa

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari kan ƙauyuka biyu a karamar hukumar Rabbah a jihar Sakkwato, sun halaka mutane
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai hare-haren lokuta daban daban, sun sace dabbobi tare da ƙona gidaje
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya tabbatar da kai hare-haren amma ya ce a yanzu suna kan bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Akalla mutane 11 suka rasa rayukansu yayin da ƴan bindigan daji suka kai sabon farmaki a kauyuka biyu da ke yankin Gandi a ƙaramar hukumar Rabbah, jihar Sakkwato.

Wata majiya daga cikin ƙauyukan da lamarin ya shafa ta tabbatar da lamarin ga wakilin jaridar Punch, inda ta bayyana cewa cikin mako ɗaya maharan suka aikata hakan.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Bom ya halaka manyan kwamandojin CJTF 2 da wasu mutum 4 a Borno

Yan bindiga sun kuma kai hari a Sakkwato.
Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kauyukan Jihar Sakkwato, Sun Kashe Mutane Hoto: Punchng
Asali: Twitter

A cewar majiyar, ƙauyukan da harin ya shafa su ne, Gidan-Buwai and Maikujera duk a ƙaramar hukumar Rabbah da ke Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya faru a ƙauyen Gidan Buwai

Mazaunin yankin mai suna, Salisu Gandi, ya ce ƴan bindigan sun kai hari ƙauyukan a lokuta daban-daban cikin mako ɗaya, sun sace dabbobi sama da 300.

Mutumin ya ƙara da bayanin cewa gungun ƴan bindiga da suka kai farmaki ƙauyen Gidan Buwai, sun shiga ne ranar Litinin da daddare suka aikata nufinsu.

"Sun tattara dabbobin mutane da suka ƙunshi shanu sama da 100, tumaki 200 da Akuyoyi da dama suka yi awon gaba da su yayin harin," in ji shi.

Salisu ya bayyana cewa ƴan bindigan da suka kai aƙalla mutane 100 a kan Babura ne suka kewaye kauyen Gidan Buwai ɗauke da muggan makamai a lokacin harin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙara kai hari kan ɗaliban jami'ar Tarayya, sun tafka ɓarna yayin da suka buɗe wuta

A cewarsa, bayan kewaye kauyen, nan take suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, suka kashe mutane da dama suka jikkata wasu.

Ya bayyana harin a matsayin mafi muni ganin yadda ‘yan fashin suka kona gidaje da dama, babura 10, da motoci biyar, yayin da mutane bakwai suka samu raunuka daban-daban.

Yadda aka kai harin ƙauyen Maikujera

Haka nan kuma a kwanakin baya, 'yan bindiga sun kai hari kauyen Maikujera, inda suka kashe mutum biyar yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban.

An kwantar da wadanda suka jikkata a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Wane mataki jami'an tsaro suka dauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ki cewa komai kan alkaluman.

Ya tabbatar da cewa hukumar ƴan sanda zata fitar da sanarwa a hukumance da zaran ta kammala bincike kan abin da ya faru, kamar yadda Pulse ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane a wurin Maulidi, 'yan bindiga sun ƙara kai ƙazamin hari a jihar Katsina

Jirgin Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Nasarawa

A wani rahoton kuma Mutanen da basu gaza huɗu ba sun rasa rayuwarsu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Litinin a jihar Nasarawa.

Ganau ya bayyana cewa waɗanda suka mutu suna hanyar zuwa taimaka wa ɗan uwansu a aikin gona lokacin da lamarin ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel