Innalillahi: Jirgin Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Arewacin Najeriya, Mutane da Dama Sun Mutu

Innalillahi: Jirgin Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Arewacin Najeriya, Mutane da Dama Sun Mutu

  • Jirgin ruwa ya ƙara gamuwa da hatsari a jihar Nasarawa ranar Litinin, aƙalla mutane huɗu sun riga mu gidan gaskiya
  • Ganau ya bayyana cewa waɗanda suka mutu suna hanyar zuwa taimaka wa ɗan uwansu a aikin gona lokacin da lamarin ya rutsa da su
  • Shugaban matasan yankin ya yi kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen ɗaukar matakan kaucewa faruwar haka nan gaba

Jihar Nasarawa - Mutanen da basu gaza huɗu ba sun rasa rayuwarsu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Litinin a jihar Nasarawa.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wannan ya sa haɗurran jirgin ruwan da ya faru a jihar a baya-bayan nan ya kai 16 jumulla.

Kwale-kwale ya ƙara yin hatsari a jihar Nasarawa.
Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Halaka Mutum Huɗu a Jihar Nasarawa Hoto: vanguard
Asali: UGC

Daga cikin mutum huɗun da suka rasu a sabon haɗarin, biyu ƴan uwan juna ne na jini watau iyayensu ɗaya yayin da sauran biyun sun fito daga ƙauyen Ubbe, ƙaramar hukumar Nassarawa Eggon.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙara kai hari kan ɗaliban jami'ar Tarayya, sun tafka ɓarna yayin da suka buɗe wuta

Idan baku manta ba makamancin wannan hatsarin ya rutsa da fasinjojin jirgin ruwa a Kogi Kungra Kamfani da ke yankin Arikiya, ƙaramar hukumar Lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan hatsarin na baya, mutane 19 ne suka rasa rayukansu yayin da aka samu nasarar ceto mutun Bakwai a raye, kamar yadda Daily post ta ruwaito.

Yadda sabon hatsarin jirgin ya faru

Ganau ya bayyana cewa mutum huɗun da suka mutu a haɗarin jirgin ranar Litinin da ta gabata, sun yi niyyar zuwa yankin ne domin taimaka wa ɗan uwansu.

A cewar shaidan gani da ido, sun taho ne da nufin zuwa yankar shinkafar ɗan uwansu yayin da hatsarin ya rutsa da su lokacin da zasu ketare kogin.

Wani dan uwa ga waɗanda suka rasu sanadin haɗarin kuma shugaban matasan yankin, Kwamared JD Congo, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba (yau).

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane a wurin Maulidi, 'yan bindiga sun ƙara kai ƙazamin hari a jihar Katsina

Ya kuma roki gwamnatin jihar Nasarawa da ta samar da matakan da ya dace domin kaucewa sake afkuwar irin haka a nan gaba.

"Ina kira ga gwamnatin jihar Nasarawa da darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar da su dauki matakan da suka dace don dakile kwararowar ruwa daga dam din Lagdo na ƙasar Kamaru."
"Bisa haka ina rokon gwamnati da ta kara kaimi wajen samar da jiragen ruwa na zamani, da rigunan ceto, da kuma rundunar ruwa domin tabbatar da tsaron mazauna yankin,” in ji shi.

Yan bindiga sun kai hari a Nasarawa

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai sabon hari a Gandu, yankin jami'ar tarayya ta Lafiya a karamar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafka ɓarna yayin harin kana suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262