Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Hari Kan Ɗaliban Jami'ar Tarayya, Sun Tafka Ɓarna Yayin da Suka Buɗe Wuta

Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Hari Kan Ɗaliban Jami'ar Tarayya, Sun Tafka Ɓarna Yayin da Suka Buɗe Wuta

  • Yan bindiga sun kai sabon hari a Gandu, yankin jami'ar tarayya ta Lafiya a karamar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafka ɓarna yayin harin kana suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa
  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna damuwarsa kan karuwar matsalar tsaro a manyan makarantun jihar

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun kai sabon hari a ƙauyen Gandu, yankin jami'ar tarayya da ke Lafia a ƙaramar hukumar Lafiya, jihar Nasarawa.

Yan bindiga sun kai harin Gandu, yankin jami'ar tarayya ta Lafia.
Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Hari Kan Ɗaliban Jami'ar Tarayya, Sun Tafka Ɓarna Yayin da Suka Buɗe Wuta Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Yayin wannan farmaki, ƴan bindigan sun yi garkuwa da wani ɗan kasuwa, kuma sun harɓi ɗalibin jami'ar da ke aji uku (300 level) a kwas din Sociology.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane a wurin Maulidi, 'yan bindiga sun ƙara kai ƙazamin hari a jihar Katsina

Yadda maharan suka ci karensu babu babbaka

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa maharan ɗauke da manyan makamai sun shiga yankin da misalin ƙarfe 8:30 na daren jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga zuwansu, ƴan bindigan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutanen yankin, daga bisani suka aikata ayyukan ta'addancinsu suka ƙara gaba.

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigan da har yanzu ba a gano ko su waye ba, sun yi garkuwa da ɗan kasuwan, suka tasa shi zuwa maɓoyarsu a cikin jeji.

Wani Ganau wanda bai son a ambaci sunansa, ya ce ɗaliban jami'ar tarayya ta Lafia da ke zaune a Gandu, ba su iya bacci ba tun ƙarfe 7:00 na dare saboda fargabar hari.

Haka nan wani ɗalibin 400 level, wanda aka kwace masa wayoyi biyu a harin, ya ce mako uku da suka wuce, wasu ƴan bindiga suka kwace wayoyin ɗalibai aƙalla 5, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, sun tafka ɓarna yayin da suka yi garkuwa da mutane

Ɗalibin, wanda ya nemi kar a ambaci sunansa, ya ce tun bayan aukuwar lamarin, ba bu wani hubbasa da jami'an tsaro suka yi na kwamuso waɗanda suka aikata hakan.

Gwamna Sule ya shiga damuwa

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kusa da manyan makarantun jihar.

Yayin da ya ke mika ta’aziyyarsa ga jami'ar kan lamarin, Gwamna Sule ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin an inganta tsaro a yankunan da daliban ke zama a wani mataki na dakile matsalar tsaro.

Yan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani rahoton na daban Miyagun ƴan bindiga sun ƙara kashe mutane a kauyen Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina ranar Litinin.

Wannan harin na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan mahara sun kai hari wurin taron Maulidi a ƙaramar hukumar Musawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel