Bayan Kashe Mutane a Wurin Maulidi, Ƴan Bindiga Sun Kara Kai Kazamin Hari a Jihar Katsina

Bayan Kashe Mutane a Wurin Maulidi, Ƴan Bindiga Sun Kara Kai Kazamin Hari a Jihar Katsina

  • Miyagun ƴan bindiga sun ƙara kashe mutane a kauyen Sayaya da ke ƙaramar hukumar Matazu a jihar Katsina ranar Litinin
  • Wannan harin na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan mahara sun kai hari wurin taron Maulidi a ƙaramar hukumar Musawa
  • A sabon harin, ƴan bindiga sun kashe akalla mutane 5 yayin da suka jikkata wasu da dama, kana suka sace wasu 7

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Mutanen da basu gaza biyar ba sun mutu, wasu da dama sun jikkata yayin da ƴan bindiga suka kai sabon mummunan hari a kauyen Sayaya, ƙaramar hukumar Matazu a Katsina.

Yan bindiga sun kai sabon hari a Katsina.
Yan Bindiga Sun Kara Kai Mummunan Hari Jihar Katsina, Sun Kashe Mutane Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Kamar yadda Channesl tv ta ruwaito, ƴan ta'addan sun kaddamar da wannan sabon harin ne ranar Litinin da daddare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Abuja, sun tafka ɓarna yayin da suka yi garkuwa da mutane

Wani jami'in tsaro da aka ɓoye sunansa, ya tabbatar da faruwar lamrin ga wakilin jaridar a wata hira ta wayar tarho ranar Talata (yau).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da wasu mutanen ƙauyen su bakwai zuwa wurin da babu wanda ya sani.

Yan bindiga sun kai hari wurin Maulidi

Lamarin dai na zuwa ne kwana guda bayan wani hari makamancin haka ya auku a karamar hukumar Musawa da ke makwabtaka da ita Matazu.

Harin na ranar Lahadi ya auku ne da misalin ƙarfe 10:00na dare, inda ƴan bindiga sun farmaki wurin shagalin bikin Maulidi a ƙauyen Rugar Ƙusa da ke yankin Musawa.

Yayin wannan hari mara daɗin ji, maharan sun kashe tare da yanka mutane 14 daga cikin mahalarta taron Maulidin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga babbar matsala, masu ruwa da tsakin PDP sun goyi bayan Ministan Tinubu

Harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne, ya dauki sama da sa'a guda, kuma ƴan ta'addan sun yi garkuwa da mutanen da ba su gaza 20 ba a harin.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindiga na isa wurin taron maulidin, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane.

Shida daga cikin wadanda aka kashe ‘yan kauyen Rugar Kusa ne, biyu kuma ‘yan Gidan Malamai ne, shida kuma sun fito ne daga kananan hukumomin Musawa da Matazu.

Mazauna kauyen Sayaya sun tabbatar da faruwar lamarin ga wakiin Legit Hausa, inda suka ce gida-gida maharan suka shiga, suka tafi da mata da kananan yara.

Wata majiya daga yankin da ta nemi a sakaya bayananta ta ce ƴan bindigan sun sace mata 15 ciki har da mai tsohon ciki haihuwa yau ko gobe da kuma ƙaramin ɗanta.

"Abun ba daɗin ji, sun shiga gida-gida, sun tafi da mata 15 ciki harda mai tsohon ciki da ɗanta, muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan abu domin ya wuce tunanin kowa," in ji ta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki a wurin taron Mauludi a Katsina, sun halaka mutum 20 da sace wasu da dama

Miyagun Ƴan Bindiga Sun Ƙara Shiga Abuja

A wani rahoton kun ji cewa Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwan juna biyu da wani mai gidan ruwan leda a yankin Bwari da ke birnin tarayya Abuja.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun kira dangin wadda suka sace, sun nemi kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262