Jihohi 10 Mafi Zaman Lafiya a Najeriya: Cikakken Jerinsu

Jihohi 10 Mafi Zaman Lafiya a Najeriya: Cikakken Jerinsu

  • Matsalar rashin tsaro a Najeriya ta zama ruwan dare inda kusan ko wani yanki na zama da ita tsawon kimanin shekaru goma yanzu
  • Sabon rahoton binciken da aka saki ranar Lahadi, 8 ga Junairu ya lissafa jihohi goma mafi zaman lafiya
  • Jihar Ekiti da ke yankin kudu maso yammacin kasar ne ya zo na daya cikin jeringiyar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yayinda Najeriya ta shiga watan farko na sabuwar shekara kuma saura wata guda zaben 2023, Najeriya na cike da tsoro da fargaba bisa matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Matsalar tsaro ta zama kayar wuya ga dukkan sassan Najeriya kuma ana fargabar gada abin yayin tsamari lokacin zabe.

Yayinda yankin Arewa maso Yamma, Arewa maso Tsakiya, da Kudu maso Yamma, ke fama da matsalar da yan bindiga masu garkuwa da mutane, yankin Kudu maso Yamma na fama da ta'addancin IPOB, sannan Arewa maso Gabas matsalar Boko Haram/ISWAP.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

Sabon binciken da Statisense ya saki ranar Lahadi, 8 ga Junairu ya bayyana adadin wadanda aka kashe a jihohin Najeriya a 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

States
Jihohi 10 Mafi Zaman Lafiya a Najeriya: Cikakken Jerinsu
Asali: UGC

A cewar rahoton da Statisense ya fitar, jihohi 10 ne kacal cikin jihohin Najeriya 36 suke da zaman lafiya.

Cikin wadannan jihohi akwai na Arewa biyar, na kudu biyar.

Jihar Ekiti ce ta ciri tuta matsayin jihar da aka samu kisan mutu 6 kacal sanadiyar rashin tsaro a tsawon shekarar 2022.

Jihar Kano, Gombe, Adamawa da Kano da Jigawa ne jihohin Arewa da suka samu shiga jerin.

Ga jerin jihohin nan:

S/NJihohiAdadin wadanda aka kashe
1Ekiti6
2Gombe12
3Adamawa17
4Kano17
5Jigawa20
6Nasarawa20
7Akwa Ibom29
8Bayelsa31
9Oyo41
10Osun46

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Ƙasa da Sakatare a Villa

Jerin Birane 5 Masu Matukar Kyau Da Kayatarwa a Nahiyar Afrika

A wani rahoton a baya kun samu bayani dangane da birane da suka fi kyau a nahiyar Afirka wacce ke dauke da dumbin mutane kimanin biliyan 1.3.

Afirka na da kasashe sama da 50 masu al'adu daban-daban da bambance-bambance. Wadannan kasashe suna da wuraren shakatawa daban-daban da kuma wurare kala-kala na bincike.

Akwai kasashe fiye da 50 a nahiyar ta Afirka kuma daga cikin birane mafi kyau akwai Cairo da ke Egypt.

Asali: Legit.ng

Online view pixel