Don Allah a Rage Farashi: Tsadar Abinci Ya Jawo Sarki Ya Ziyarci Kasuwannin Gari

Don Allah a Rage Farashi: Tsadar Abinci Ya Jawo Sarki Ya Ziyarci Kasuwannin Gari

  • Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu ya ziyarci kasuwanni domin ganin yadda farashin kayayyakin masarufi su ke
  • Mai Martaban ya roki ‘yan kasuwan Bauchi su hakura da karamar riba domin al’umma su iya samun abincin da za su ci
  • A halin yanzu mutane da-dama su na kukan kayan abinci sun yi tsada a lokacin da man fetur ya yi tsadar da ba a taba gani ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu ya kai ziyarar ba-zata zuwa wasu manyan kasuwannin da ke cikin kasarsa.

Rahoton Daily Trust ya ce Sarkin Bauchi ya yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma da su guji tsawwala farashin kaya a halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Mai martaba Rilwanu Adamu ya bayyana haka ne ganin tsadar rayuwan da musamman talakawa ke fuskanta kafin sayen abin da za a ci.

Sarkin Bauchi
Sarkin Bauchi a kasuwa Hoto: Ansar Emirates Photography
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai martaba Sarkin Bauchi ya je kasuwa

A yayin ziyarar da ya kai, Basaraken ya tattauna da masu kaya domin jin farashin hatsi, ganye da sauran kayan abinci a kasuwanninsa.

Jaridar ta ce a matsayinsa na Uba, Sarkin ya yi kira ga ‘yan kasuwa su rika saukakawa al’umma ta hanyar hakura da cin karamar riba.

Mai Martaban ya ce idan aka yi araha ne marasa hali da sauran masu karamin karfi za su iya cin abinci tare da yi masu addu’ar samun budi.

Man fetur: Sarki ya yabi 'yan kasuwan Bauchi

A sakamakon tashin kudin mota, Sarkin ya jinjinawa ‘yan kasuwa game da yadda su ka jurewa janye tallafin man fetur da aka yi a kasar.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

Da ya shiga kasuwar Wunti, Leadership ta ce Sarkin Bauchi ya fadawa masu saida ganye cewa lafta farashi ba abin kwarai ba ne a addini.

‘Yan kasuwan sun yi wa Sarki alkawari ba za su cika farashin kaya ba saboda a iya saye.

Hira da 'dan kasuwa a Bauchi

Malam Shamsuddeen Ahmad Rufai ‘dan kasuwa ne a garin Bauchi, ya shaida mana cewa Sarki ya yi kira ga masu kaya su ji tsoron Allah SWT.

Mai martaba ya yi nasiha ga masu yawan kara farashi babu gaira babu dalili, ya kuma yi gargadi a kan tauye mudu da rashin fitar da zakkah.

‘Dan kasuwan ya fadawa Legit cewa daga baya shugabannin babban kasuwa na garin Bauchi sun je fada sun zauna da Mai martaba Sarki.

A cewarsa, wannan yunkurin da Sarki ya yi zai iya yin tasiri, wasu masu kayan za su dauki hudubarsa domin akwai masu tsawwala farashin kaya.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Tattalin arziki ya fara gyaruwa

Duk da jigo ne shi a jam'iyyar PDP, mu na da labari Ben Murray Bruce ya ce tattalin arzikin Najeriya yana gyaruwa a gwamnatin Bola Tinubu.

Tsohon Sanatan Bayelsa ya yabi manufofin da aka kawo bayan Muhammadu Buhari ya sauka, ya ji dadin manufofin da aka kawo a bankin CBN

Asali: Legit.ng

Online view pixel