Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago na Son Gwamnati ta Biya ₦615,000 a Wata

Mafi Karancin Albashi: Kungiyoyin Kwadago na Son Gwamnati ta Biya ₦615,000 a Wata

  • Kungiyar kwadago ta TUC ta ce har yanzu ana tattaunawa kan yadda za a bullowa batun mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya
  • Shugaban kungiyar Festus Osifo da ya bayyana hakan ya ce yanzu haka su na tattaunawa da wakilan gwamnati domin cimma matsaya
  • Kungiyoyin ma'aikata na NLC da TUC na bukatar gwamnatin tarayya ta biya ma'aikatan kasar nan N615,000, amma har yanzu ana duba batun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Kungiyar kwadago ta TUC ta ce har yanzu ana tattaunawa kan mafi karancin albashi a tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Shugaban TUC, Kwamared Festus Osifo ne ya bayyanawa manema labarai hakan a Abuja.

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya shawo kan matsalar da ta kawo dogon layi a gidajen mai

Kungiyar kwadago ta TUC ta ce zai yi wahala a bayyana mafi karancin albashi kwanan nan
Kungiyoyin kwadago na ganin ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata fiye da N600,000 Hoto:@NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Ya ce zai yi matukar wahala a ayyana matsaya kan mafi karancin albashin a ranar ma'aikata da ake gudanarwa a 1 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Akwai tabbacin ba za a bayyana mafi karancin albashi a ranar 1 ga watan Mayu ba. Sai dai idan gwamnatin tarayya na son biyan ma'aikata ₦500,000 a matsayin mafi karancin albashi."

A rahoton da jaridar Punch ta wallafa, Kwamared Festus Osifo ya ce har yanzu su na tattaunawa da kungiyar kwadago ta NLC da wakilan gwamnati domin samar da matsaya.

Kungiyoyin kwadago sun cimma matsaya

A cewar kwamared Osifo, kungiyarsa da ta NLC sun cimma matsaya kan albashin da su ke ganin ya fi kyautuwa gwamnati ta biya ma'aikata.

Ya ce idan son samu ne, a biya ma'aikatan mafi makarancin albashin N615,000, daga ₦30,000 da ake biya a yanzu.

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

Shugaban ya ce tun da fari sun nemi gwamnati ta biya N447,000 kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Amma bayan sa labule da NLC su ka ga bukatar neman a biya ma'aikatan kasar nan N615,000 sai dai babu tabbacin a sanar da karin kafin 1 ga watan Mayun bana.

Kungiyar kwadago ta sabunta bukatunta

Mun kawo mu ku a baya cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce akwai sabbin bukatun da ya kamata gwamnatin kasar nan ta waiwaya domin jin dadin ma'aikatan Najeriya.

Daga cikin bukatun akwai samar da dangantaka mai kyau tsakaninsu da gwamnati, aiwatar da mafi karancin albashi, biyan basussukan kudin fansho da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel