Sarkin Bauchi ya Tsige Mutumin Atiku daga Sarautar Waziri a Dalilin Rikici da Gwamna

Sarkin Bauchi ya Tsige Mutumin Atiku daga Sarautar Waziri a Dalilin Rikici da Gwamna

  • Sarautar Wazirin Bauchi ta tashi daga kan Alhaji Muhammadu Bello Kirfi bayan an tunbuke shi
  • Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya fitar da wasika a madadin masarauta cewa an yi waje da Bello Kirfi
  • Sarkin Bauchi ya amince da hakan bayan samun Waziri da rashin yi wa Gwamna biyayya

Bauchi - Masarautar kasar Bauchi ta sauke Alhaji (Dr) Muhammadu Bello Kirfi daga kan kujerar da yake kai, sannan kuma an cire masa rawaninsa.

Kafin a dauki wannan mataki, Daily Trust ta ce Muhammadu Bello Kirfi shi ne Wazirin Bauchi kuma yana cikin manyan ‘yan majalisar fadar Sarki.

An tunbuke Wazirin Bauchi daga kujerarsa ne bayan samun shi da rashin ladabi da rashin girmama Mai martaba Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed.

Rahotanni sun tabbatar da Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu ya amince da wannan mataki da masarautarsa ta dauka a makon nan.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi Ya Kori Wazirinsa, Na Hannun Daman Atiku, Bello Kirfi, Kan Rashin Biyayya Ga Gwamnan Bauchi

Sakataren fadar Sarkin Bauchi, Alhaji Shehu Mudi Muhammad ya fitar da wasikar tunbuke Mai girma Wazirin a ranar Talata, 3 ga watan Junairun 2023.

Korafin Gwamnatin Bauchi

Wasikar tayi nuni ga wata takarda mai lamba MLG/LG/S/72/T da ma’aikatar kananan hukumomi ta aikowa fadar a ranar 30 ga watan Disamba 2022.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sarkin Wazirin Bauchi
Bala Mohammed da Wazirin Bauchi, Bello Kirfi Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wannan takarda ta zargi Muhammadu Bello Kirfi da rashin biyayya ga Mai girma gwamnan jihar Bauchi da gwamnatinsa, don haka aka tunbuke shi.

Masarautar ta ce abin da wasikar gwamnatin Bauchi ta kunsa shi ne a cire masa rawani. A karshe, Shehu Mudi ya yi wa Bello Kirfi fatan alheri nan gaba.

Jaridar ta ce Kirfi ya rike Ministan harkokin kasar waje a gwamnatin Shehu Shagari da kuma Ministan harkokin musamman a lokacin Olusegun Obasanjo.

A lokacin da masarautar ta fitar da wannan wasika, Bello Kirfi ba ya Najeriya. ‘Yanuwansa sun fadi cewa sai ya dawo watakila za a ji daga bakinsa.

Kara karanta wannan

Sojin Sama Sun Sheke Kwamandojin Boko Haram 3, Mayaka 30, Sun Jikkata 40 a Wata Jahar Arewa

“Idan ya dawo Bauchi, danginsa za su yi taro, su dauki matakin maida martani ko akasin haka.”

- Dangin Bello Kirfi

“Bala Must go”

Daily Nigerian ta ce ana zargin tsohon Wazirin na Bauchi yana cikin gungun da suka taso Bala Mohammed a gaba, su na neman hana shi zarcewa.

Sauran ‘yan siyasan da ke yakar Gwamnan sun hada da Ahmad Adamu Mu’azu da tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel