Mai Magani Ya Dirkawa Wani Harsashi Har Lahira Yayin Gwada Maganin Bindiga a Bauchi

Mai Magani Ya Dirkawa Wani Harsashi Har Lahira Yayin Gwada Maganin Bindiga a Bauchi

  • Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun cafke wasu mutane biyu kan zargin kisan wani matashi yayin gwada maganin bindiga
  • Marigayin Muhammad Ali mai shekaru 43 ya tafi da mai maganin gargajiya da wasu don gwada maganin bindigan a kansa
  • Kakakin rundunar a jihar, Ahmed Wakili shi ya tabbatar da haka a yau Talata 7 ga watan Nuwamba a birnin Bauchi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi – Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wasu mutane biyu kan zargin gwada maganin bindiga a kan wani mutum.

Marigayin Muhammad Ali mai shekaru 43 ya rasa ransa yayin da mai maganin gargajiya ke gwada maganin bindigan a kansa, cewar NewsNow.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Wani mutum ya rasa ransa yayin gwada maganin bindiga a Bauchi
'Yan sanda sun cafke mai magani kan kian wani a Bauchi. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene ake zargin mutanen da aikata wa?

Ali wanda ke kauyen Bursari a karamar hukumar Zaki ya tafi da mutanen hudu ne cikin daji don gwada maganin ko zai hana harsashin bindiga yi ma sa illa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Ahmed Wakil shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau Talata 7 ga watan Nuwamba.

Ya ce jami’ansu sun cafke mutane biyu daga cikinsu yayin da sauran su ka tsere inda ya ce sun bazama farautarsu, Daily Post ta tattaro.

Wane shawara ‘yan sanda su ka bayar?

Ya ce:

“A ranar 31 ga watan Oktoba mun samu rahoton cewa wani mai suna Danladi Ya’u mai shekaru 28 da wasu sun tafi da Muhammad Ali don gwada maganin bindiga a daji.
“A kokarin gwada bindigar, Muhammad mai shekaru 43 ya rasa ransa bayan an harbe shi da ita.”

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

Ahmed ya shawarci al’umma da su guji bari mutane su na amfani da su wurin gwada irin wannan magunguna a kansu inda ya ce wannan ya zama darasi.

‘Yan sanda sun cafke mata kan zargin kisa a Bauchi

A wani labarin, jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun kama wata mata kan zargin hallaka ‘yar kishiyarta.

Matar mai suna Khadija Adamu ta bayyana cewa ba da gangan ta aikata hakan ba inda ta ce iyayen yarinyar sun yafe mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel