Kogi: "Ni Ake Nema a Kashe" Ɗan Takarar Gwamna Ya Tona Shirin Gwamnan APC a Jihar Arewa

Kogi: "Ni Ake Nema a Kashe" Ɗan Takarar Gwamna Ya Tona Shirin Gwamnan APC a Jihar Arewa

  • Murtala Ajaka ya zargi Gwamna Yahaya Bello da amfani da wasu jami'an tsaro domin cimma burinsa na raba shi da duniya
  • Ɗan takarar gwamnan jihar Kogi a inuwar SDP ya ce manufar harin da aka kai Dekina shi ne a kashe shi amma ya tsallake
  • Ya bayyana cewa Gwamna Bello na kokarin kakabawa mutane magajinsa ko ta halin ƙaƙa amma al'ummar Kogi sun juya masa baya

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Ɗan takarar Gwamnan jihar Kogi a zabe mai zuwa a inuwar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka, ya yi zargin cewa ana kulle-ƙullen ganin bayansa.

Mista Ajaka ya yi wannan zargin ne yayin da yake maida martani kan harin da aka kai a ƙaramar hukumar Dekina a jihar Kogi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

Dan takarar gwamna a inuwar SDP, Murtala Ajaka.
Zaben Kogi: "Ina Cikin Waɗanda Ake Harin Kashe Wa" Ɗan Takarar SDP Hoto: Murtala Ajaka
Asali: UGC

Yayin hira da gidan talabijin na Channels a cikin shirinsu na siyasa a yau, ɗan takarar ya bayyana cewa yana zargin ana nemansa da nufin a raba shi da duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kai ziyara hedkwatar rundunar ƴan sandan Najeriya da ke birnin tarayya Abuja domin kai ƙorafi da nuna adawarsa da abubuwan da ke faruwa.

Mu uku su ke nema su kashe - Ajaka

A ruwayar Daily Trust, Ajaka ya ce:

"Ana kai hare-haren da umarnin kwamanda ɗaya, ku duba motocinsu, jami'an Sibil Defens da suke amfani da su ba ƴan jihar Kogi bane, sun zo ne saboda zaɓe kaɗai."
"Wannan ya afku ne a ƙaramar hukumar Dekina, nan ne wurin da na saba zama duk lokacin da na je Dekina. Manufarsu su kama ni, darektan kamfen ɗina da shugaban APC na shiyyar, Ahmad Ata, su kashe mu."

Kara karanta wannan

Nasarar Tinubu: Peter Obi ya yanke shawara kan sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

"Gwamna ya ce baya son ganina a raye, su kai ni Kotu mana, zan yi cikakken bayani kuma ina da kaset mai ɗauke da sautin murya."

Manufar Yahaya Bello kan al'ummar Kogi

Ɗan takarar na SDP ya ƙara da cewa Gwamna Yahaya Bello na son ƙaƙaba wa al'ummar jihar Kogi wanda zai gaje shi, inda ya ce mutane na goyon bayan takararsa.

"Gwamna na ƙoƙarin ta kowane hali ya ƙaƙaba wa mutanen jihar Kogi wanda zai gaje shi, su kuma mutane ba su son sake ganin Yahaya Bello har abada."

An kara kai harin a yankin jami'ar Tarayya

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai sabon hari a Gandu, yankin jami'ar tarayya ta Lafiya a karamar hukumar Lafia ta jihar Nasarawa.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafka ɓarna yayin harin kana suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel