Tinubu Ya Bayyana Dalilin Cire Tallafin Man Fetur, Ya Ce Wasu Tsirarun Mutane Ke Amfani Da Shi

Tinubu Ya Bayyana Dalilin Cire Tallafin Man Fetur, Ya Ce Wasu Tsirarun Mutane Ke Amfani Da Shi

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sanya shi dakatar da ba da tallafin man fetur
  • Tinubu ya ce kuɗaɗen tallafin man fetur da ake biya a baya na zurarewa ne zuwa asusun bankunan wasu tsirarun mutane
  • Ya ƙara da cewa muddun akwai irin waɗannan mutanen a wuri, to ba za a samu ci gaban da ake tsammani ba

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilan da suka sa ya kawo ƙarshen tsarin bayar da tallafin man fetur a Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa dole ne a kawo ƙarshen tsarin biyan tallafin man fetur, saboda ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyansa ba.

Ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da jawabi ga 'yan ƙasa, wanda aka haska shi kai tsaye a gidan talabijin na NTA da yammacin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tallafi: Tinubu Ya Yi Wa Ɗaliban Najeriya Gagarumin Aiki Domin Saukaka Rayuwarsu

Tinubu ya bayyana dalilin cire tallafin man fetur
Tinubu ya ce wasu 'yan tsirarun mutane ne ke amfana da tallafin man fetur. Hoto: Comr Abba Sani Pantami
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya bayyana yadda ya kamata a riƙa amfani da kuɗaɗen tallafin

Tinubu ya ce kamata ya yi ayi amfani da tiriliyoyin nairori da ake kashewa duk shekara a kan tallafin, wajen inganta fannin kiwon lafiya, sufuri, makarantu, gidaje, tsaron ƙasa da dai sauransu.

Ya ƙara da cewa a asusun bankin wasu 'yan tsirarun mutane kuɗaɗen tallafin fetur ɗin ke shigewa.

Sannan Tinubu ya bayyana cewa waɗannan mutanen sakamakon maƙudan kuɗaɗen da suka tara, sun zama babbar barazana ga tattalin arziƙin ƙasa.

Tinubu ya ƙara da cewa, Najeriya ba za ta taɓa samun ci gaban da ake tsammani ba muddun akwai irin waɗannan mutanen a wuri saboda irin tasirin da suke da shi.

Buhari ma ya hango buƙatar cire tallafin tun kafin ya sauka

Tinubu a cikin jawabin nasa ya ce bai kamata wasu ya zamo cewa wasu mutane 'yan kaɗan ne suka tattare arziƙin 'yan ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Boka Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi Layar Zana Ba Yayin Da Masu Garkuwa Suka Zo Sace Shi

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta ga haɗarin da ke cikin tallafin, wanda hakan ya sa ba ta yi wani tanadi a cikin kasafin kudin 2023 domin tallafin da ya ƙare a watan Yuni ba.

Ya ce cire tallafin da gwamnatinsa ta yi ya zama wajibi a halin da ake ciki kamar yadda jaridar The Punch ta tattaro.

Tinubu ya gargaɗi manyan makarantu kan ƙarin kuɗaɗen makaranta

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa manyan makarantu na gaba da sakandire.

Tinubu ya gargaɗesu kan ƙara kuɗaɗen makaranta babu gaira babu dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel