So Gamon Jini: Daga Yanke Mata Farce, Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Soyayya da Mai Yankan Kumba

So Gamon Jini: Daga Yanke Mata Farce, Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Soyayya da Mai Yankan Kumba

  • Wata mata ‘yar Najeriya ta girgiza al’ummar kafar sada zumunta yayin da ta nuna bidiyon wani mai yankan farce
  • Budurwar ta yi masa bidiyo ne taya murmurshi a lokacin da ya yanke mata farce, inda tace ita fa tana kaunarsa
  • Yayin da wasu ke bayyana ra’ayin ya kamata ta biya shi kudinsa, wasu sun ce yaba masa bisa kwarewa a aikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta girgiza intanet, ta bayyana kaunarta ga wani matashi mai sana’ar yankan farce.

A wani bidiyon da aka gana a Tiktok, budurwar ta nuna lokacin da matashin ke yi mata yankan farce cikin kwarewa.

Matashin ya yi murmushi kana ya yi mata wani kallo. Budurwar mai suna @Niffynelly sai ta dauko wayarta tare da daukar bidiyon selfie tare da matashin.

Kara karanta wannan

“Kasuwa ta yi kyau”: Mabaraciya ta siya soyayyar kaza, ta darje ta zabi wanda take so

Daga yankan kumba budurwa ta haukace da son matashi
Budurwa ta ce tana son mai yankan farce | Hoto: @niffynelly
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ki biya shi kudansa

Mutane da dama a kafar sada zumunta sun yi dariya, inda suka bayyana bukatar ta biya shi kudinsa kawai, ban da wayau.

Wasu sun yabawa matashin bisa aiki da kwarewa, wasu kuwa suka bayyana cewa kyakkyawan matashi ne

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

@AbdulBasit67:

"Dole dai ki biya shi bayan nan sai ki nemi ya yanke miki a kyauta.”

kassimabdullai:

"Ina taya ki murna ‘yar uwa kada ki damu da abin da mutane za su ce kawai ki bi zuciyarki.”

Ejeagu Justus:

"Wannan dai yaro ne don Allah kada ki bata shi.”

evil 4kt:

'Wannan kyakkyawan yaro ne kuma da gani idan ya samu rayuwa mai kyau zai ma fi haka kyau, ina maku addu’a.”

Tobeelorbah:

"Abin dariya yanzu wani ya yanke min farce ko kallo na ma bai yi.”

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar a runtuma kame, 'yan kauye sun yi wa alkali jina-jina a jihar Gombe

Black beauty:

"Matashi na kallonki kina dariya kawai ki biya shi kudinsa cif-cif.”

Kudin da mai yankan farce ke samu

A bangare guda, an yi fira da mai yankan farce, ya fadi irin kudaden da suke samu a wannan sana'ar da wasu suka raina.

A cewar Ibrahim Kabiru, yakan samu kudin da basu yi kasa da N45,000 duk wata a sana'ar da yake yi a jihar Edo.

Sana'ar yankan farce dai sana'a ce da ake samun almajirai ke yi a Arewacin Najeriya, galibi Hausawa ke yinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.