Hukuncin yanke farce da aski ga mai Layya a wannan wata

Hukuncin yanke farce da aski ga mai Layya a wannan wata

- Mun kawo hukuncin aski ga mai niyyar yin Layya

- Har da kuma yanke farata a farkon wannan wata

- A wannan wata ne ake Layya na bikin Sallah

A yau kuma mun shiga zauren Musulunci inda mu ka kawo hukuncin aski ga mai niyyar yin Layya.

Hukuncin yanke farce da aski ga mai Layya a wannan wata
Bikin Sallar idi a Najeriya

Akwai hadisi daga Nana Umm Salma RA da tace Annabi SAW yace da zarar an shiga wannan wata na Dhul Hajj ka da mutum ya yanke akaifar sa ko ya aske sumar sa har sai ya yanka dabbar sa. A wata ruwayar ma aka hada da cewa sa wani abu na fatar jikin sa.

KU KARANTA: Sultan ya goyi bayan Gwamnati

Sai dai akwai wani Hadisin daga Nana Aisha ita ma RA inda tace su na aikin Hajji da Manzon Allaah SAW kuma ya umarce ta da ta tsefe gashin ta bayan ta tsefe kitson ta. Duk da haka sai dai ita ma ba za ta datse farata ba muddin za tayi Layya sai ta yanka dabbar ta.

A farkon wannan watan ne ake samun Ranar Arafah. Duk wani Mahajjaci a wannan rana ya dukafa ana kuma neman rahamar Allah. Ana son azumi ga wadanda ba su je Hajji ba wanda ke kankare zunuban shekara biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kayan masarufi sun yi tsada

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng