Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata

Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata

- Wani mai sana'ar yankan farce ya bayyana irin tagomashin da yake samu a sana'r tasa ta yankan farce

- Ya ce akalla yakan samu sama da N1,500 a kowacce rana, kuma yakan hada N45,000 a wata

- Ya bayyana yadda ya yi kaura takanas tun daga jihar Sakkwato har jihar Edo don yin sana'ar

Wani matashi mai shekaru 19 dake sana’ar yankan farce a birnin Benin na jihar Edo, Ibrahim Kabiru ya ce ya kan samu akalla N1,500 a kullum, jumillar N45,000 a kowane wata, Aminiya ta ruwaito.

Ibrahim, a cikin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ce sana’ar na taimaka masa matuka wajen biyan bukatunsa na yau da kullum.

Ya ce ya yi kaura ne takanas tun daga jihar Sakkwato zuwa jihar ta Edo domin yin sana’ar yankan farce.

A cewarsa, duk da yake yana shan wahala matuka wajen yawo a cikin birnin yana neman kwastomomi, amma abin da yake samu yana isarshi.

KU KARANTA: Na Fara Addu’a Allah Ya Tsige Shugaba Buhari Daga Mulki, in ji Fasto Wale Oke

Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata
Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ibrahim ya shaida wa NAN cewa a baya yana sana’ar noman masara ne amma karancin jari ya sa tilas ya nemi wata sana’ar.

Ya ce ya kan karbi N100 a kan kowanne yankan farce da kankara, yayin da idan yanka ne zalla ba kankara ya kan karbi N50.

Mai yankan farcen ya ce jarin da ake bukata domin fara sana’ar bai wuce N1,000 ba domin sayen almakasa, soso, ruwa da kuma sabulu.

Da aka tambaye shi ko yana da niyyar komawa harkar noman idan ya samu jari sai ya ce eh, inda ya ce noma a yanzu dole yana bukatar jari.

Ya ce kasancewar bai yi karatun boko ba, sana’ar yankan farcen kawai zai Yankan farce, Edo, Beniniya yi sai kuma ta noman.

KU KARANTA: Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC

A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya hana wasan Tashe na gargajiya da ake gudanarwa a cikin watan Ramadan, gidan talabijin Channels ya ruwaito.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, al'adu, da harkokin cikin gida, Abdulkarim Yahaya Sirikathe ya fitar, haramcin na zuwa ne kwanaki 15 kacal bayan fara azumin Ramadana biyo bayan wasu rahotannin tsaro da suka jawo hakan.

Gwamnatin jihar ta kuma umarci jami'an tsaro a jihar da su kamo duk wanda aka samu da keta umarnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.