Akwai Yiwuwar a Runtuma Kame, ’Yan Kauye Sun Yi Wa Alkali Jina-Jina a Jihar Gombe

Akwai Yiwuwar a Runtuma Kame, ’Yan Kauye Sun Yi Wa Alkali Jina-Jina a Jihar Gombe

  • An ruwaito yadda wasu mazauna kauye suka kai farmaki kan wasu ma’aikatan kotu a Balanga, jihar Gombe
  • An kuma bayyana yadda rikicin gona ya kai ga zuwa gaban kotu, inda ya kai ga yiwa alkali da ma’aikatansa kaca-kaca
  • Ba sabon abu bane a samu hari ko farmaki a yankin Arewa, hakan na kokarin zama ruwan dare game duniya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Gombe - An bayyana zargin cewa, wasu ‘yan kauye sun kai farmaki kan alkali a yankin Degri da ke karamar hukumar Balanga a jihar Gombe.

Wadanda ake zargin an ce sun farmaki alkalin Babban Kotun Yanki na III, Ayuba Buba-Dalas, Barr Usman Yahaya da wani ma’aikacin kotun.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

An yiwa alkali duka a Gombe
An yiwa alkali da lauya duka a Gombe | Hoto: @MobilePunch, GettyImages
Asali: Twitter

Majiyar jaridar Punch ta tattaro cewa, akan samu sabani kan gonaki a yankin, inda ake warwarewa a gaban kotun da ke garin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya aka kai farmakin?

An ruwaito cewa, a wannan karon, mai shari’a Buba-Dalas ya yi kokarin zuwa da kansa don gwada fadi da tsawon wata don raba rikicin da aka kawo gabansa.

Wani ganau ya bayyana cewa, an farmaki ma’aikatan kotun ne a daidai lokacin da ‘yan kauyen suka hango suna zuwa yankin.

Kungiyar lauyoyi ta Najeriya reshen jihar Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin sakatarenta na yada labarai, Bashir Abdullahi a ranar Lahadi.

Ba sabon abu bane

Rikicin gona na daya daga abin da ke ba da ciwon kai a yankunan karkara, akan samu kashe-kashe a wasu yankunan da gajin hakuri ya kai ga daukar doka a hannu.

Kara karanta wannan

So gamon jini: Daga yanke mata farce, kyakkyawar budurwa ta fada soyayya da mai yankan kumba

Baya ga rikicin gonaki, akan samu ‘yan ta’adda da ke kai farmaki kan su kansu manoma a yankuna daban-daban an Arewacin Najeriya.

Rikicin manoma ya kai ga kisa

A wani labarin, an samu barkewar rikici a tsakanin manoma da makiyaya a kauyen Kwanga cikin karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban karamar hukumar Ngaski, Alhaji Abdullahi Buhari Warah, ya ce kisan da wasu mutane da ake zargin makiyaya ne suka yi wa wani manomi a gonarsa ne ya sanya wasu fusatattun mutane suka kai harin ramuwar gayya a wani matsugunin Fulani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.