Jama’a Sun Yi Cacar Baki Yayin da Budurwa Ta Amarce da Hoton Ango da Baya Nan, Bidiyon Ya Yadu

Jama’a Sun Yi Cacar Baki Yayin da Budurwa Ta Amarce da Hoton Ango da Baya Nan, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani bidiyo daga shagalin bikin wani ango da baya nan ya bayyana a intanet kuma ya haddasa cece-kuce tsakanin yan soshiyal midiya
  • A madadin angon da baya nan, an yi amfani da hotonsa a wajen shagalin bikin, lamarin da ya bai wa wasu yan Najeriya mamaki
  • Yadda amaryar ta dungi yi da hoton a bidiyon bai yi wa yan mata da dama ba yayin da suka bayyana ra'ayoyinsu kan haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jama'a sun yi cece-kuce a kan bidiyon shagalin bikin da aka yi tsakanin wani ango da baya nan da amaryarsa yar Najeriya.

Wani mai amfani da dandalin X mai suna @Folasheycrown22, ya yada bidiyon kan dandalin dauke da tambaya.

An sha shagalin bikin amarya ba ango
Jama’a Sun Yi Cacar Baki Yayin da Budurwa Ta Amarce da Hoton Ango da Baya Nan, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @Folasheycrown22
Asali: Twitter

Kamar yadda rubutun da ke jikin bidiyon ya nuna, angon baya nan kuma hakan ne yasa amaryar ta yi amfani da hotonsa a madadinsa.

Kara karanta wannan

Wani dan Najeriya ya gano yaransa 4 ba nashi bane bayan gwajin DNA, ya koka a bidiyo mai tsuma rai

A cikin bidiyon, amaryar ta sumbaci hotonsa kamar yana nan sannan ta durkusa a gabansa, abun da sam bai yi wa wasu yan mata dadi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu yan mata sun yi korafi cewa ba za su iya yin aure ango baya nan ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan auren angon da baya nan

@Oldynamo18 ta ce:

"Ya yi kama da bikin mutuwa."

@Azul_Eps ta yi martani:

"Abun bai yi ma'ana ba ko kadan amma idan akwai kwakkwaran dalili. Toh ya yi kyau."

@momentswtbreezy ta ce:

"Wato, zan dunga rawa da kaina sannan na dunga yi tsare0tsaren baikon ni kadai? Gara ace ban yi bikin ba gaba daya."

@marie_mimmie ta ce:

"Dole ne sai sun yi shagalin bikin??? Da kawai ya tura mutanensa da sadaki sannan ya hallara ta yanar gizo..."

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

@selormofori42 ya ce:

"Wa ke aure a bayan idona. Bikin da ban taba sanin da shi ba."

Magidanci ya gano yaransa ba nasa bane

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna, Olarenwaju Kolawole, ya bayyana cewa yara hudu da matarsa ta haifa masa duk ba nasa bane.

Kolawole ya ba da labarinsa a tashar Kokoro Alate, wani shirin gidan radiyo na Yarbanci, yana mai cewa ya gano hakan ne bayan ya yi masu gwajin DNA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel