Abin da Shugaban EFCC, Gwamnoni, Buratai Suka Fadawa Buhari da Aka Hadu a Saudi

Abin da Shugaban EFCC, Gwamnoni, Buratai Suka Fadawa Buhari da Aka Hadu a Saudi

  • Gwamnonin jihohin Borno da Yobe sun bi shugaban kasa zuwa Saudi Arabiya, sun tattauna da shi
  • Muhammadu Buhari ya hadu Zababben Gwamnan Katsina, Dikko Radda da Tukur Buratai a Makkah
  • Shugaban EFCC ya sanar da Buhari shirin da suke yi na gurfanar da wasu a kotu kan laifuffukan zabe

Saudi Arabia - A yayin da yake kasar Saudi Arabiya tare da wasu jami’an gwamnatin Najeriya, Muhammadu Buhari ya hadu da wasu Gwamnonin jihohi.

Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya yi zama da Mai Mala Buni da Babagana Umara Zulum a fadar Sarkin Makkah.

Mai magana da yawun shugaban na Najeriya ya ce baya ga Gwamnonin Yobe da Borno, Umar Dikko Radda ya samu damar ganin Buhari a inda aka sauke shi.

Kara karanta wannan

Zababben Shugaban Kasa, Tinubu Ya Shiga Cikin Mutum 100 da Suka Fi Tasiri a Duniya

Sauran wadanda suka hadu da Buhari domin fada masa halin da ake ciki kan batun zabe da aka karasa da wasu batutuwan dabam sun hada da Tukur Buratai.

Dr. Dikko Radda da Tukur Buratai

Dr. Dikko Radda shi ne zabababben Gwamnan jihar Katsina, mahaifar shugaban kasar shi kuma Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya rike hafsun sojojin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Premium Times ta ce shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa da Abike Dabiri-Erewa ta NIDCOM mai kula da 'yan Najeriya masu ci-rani sun zauna da shugaban kasar.

Buhari
Shugaban Najeriya a Makkah Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Jawabin Shugaban kasa

Bayan ya saurare su, Garba Shehu ya ce uban gidansa ya ce duk nasarorin da Najeriya ta samu a yau, a dalilin karfin damukaradiyya da hukumominta ne.

Gwamna Mala Buni da Gwamna Zulum sun ce sun ji dadin yadda gwamnati mai barin mulki ta kawo karshen Boko Haram, aka samu zaman lafiya a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Aikin Umrah Cike Da Tsaro a Garin Makkah

Guardian ta ce gwamnoni sun yi alkawarin taimakawa al’umma tare da yi wa shugaban biyayya.

Shi kuwa shugaban hukumar EFCC ya zo ne da bayanin mutanen da ake kokarin cafkewa bisa zargin tafka magudin zabe, yake cewa sun shirya kai su kotu.

Kamar yadda hotuna daga shafin Buhari Sallau suka nuna, bayan wannan zama, Isa Ali Pantami da sauran ‘yan tawagar sun yi sallar azahar tare a kasa mai tsarki.

Aisha Binani ta tafi kotu

Idan Sanata Aisha Binani ta dace a kotu, rahoto ya zo cewa Alkali zai bada umarnin dakatar da tattara zaben Adamawa wanda ya jawo rudani a Najeriya.

Lauyan Aisha Binani, Hussain Zakariyau, SAN ya yi karar INEC, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da Jam’iyyar PDP da hukumar INEC a kotu da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel