Mutum 11 Sun Rasu Wasu 10 Sun Samu Raunuka a Wani Kazamin Hatsarin Mota a Jihar Kebbi

Mutum 11 Sun Rasu Wasu 10 Sun Samu Raunuka a Wani Kazamin Hatsarin Mota a Jihar Kebbi

  • An samu asarar rayukan mutum 11 da ke cikin wata babbar mota bayan ta gamu da hatsari a jihar Kebbi
  • Mummunan hatsarin motan wanda ya auku bayan babbar motar ta yi tunguragutsi a kan titi, ya jikkata mutum 10
  • Babbar motar dai tana ɗauke ne da wake da fasinjoji domin zuwa birnin Ibadan na jihar Oyo lokacin da ta gamu da hatsarin

Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kebbi - Aƙalla fasinjoji 11 ne suka mutu inda wasu 10 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Hatsarin wanda ya auku a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, ya rutsa da wata babbar mota ƙirar Volvo DAF mai lamba KW 230 SKK, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Wasu matasa 2 sun jefa kansu a babbar matsala kan motar simintin Ɗangote

Hatsarin mota ya ritsa da fasinjoji a Kebbi
Babbar motar da hatsarin ya auku da ita Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa motar dai wani mutum mai suna Sule mai shekara 40 da haihuwa daga ƙaramar hukumar Gada ta jihar Sokoto, ke tuƙa ta, rahoton Ripples Nigeria ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin motar ya auku

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami'an ƴan sanda na sashen Shanga sun kai ɗauki kan mutanen da suka jikkata.

A kalamansa:

"Motar wacce ke ɗauke da fasinjoji da buhunan wake ta taho ne daga Sokoto zuwa Ibadan jihar Oyo. Da isa ƙauyen Giron Masa, ƙaramar hukumar Shanga, sai motar ta ƙwace wa direban inda ya rasa yadda zai yi. A sakamakon haka, ta yi tunguragutsi, inda fasinjoji 21 kuma suka samu raunuka daban-daban."

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Luguden wutar sojojin Najeriya ya halaka ƴan ta'adda sama da 160 a jihohin arewa 2

"Bayan samun rahoton, tawagar ƴan sanda daga Shanga ta garzaya wurin da lamarin ya auku, inda suka kwashe waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Shanga domin yi musu magani.
"Likitan ya tabbatar da mutuwar mutum 11, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ke karɓar magani."

A cewar Abubakar, kwamishinan ƴan sandan jihar, Chris Aimionowane, ya jajantawa iyalan fasinjojin da suka mutu, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan.

Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 12

A wani labarin kuma, wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Funtua-Gusau ya salwantar da rayukan mutum 12.

Hatsarin motar dai ya auku ne bayan wata motar bas ɗauke da fasinjoji ta ƙwace inda ta yi kan wata babbar mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel