Gwamnan PDP da Kujerarsa Ke Tangal-Tangal Ya Nemi Afuwar Al'ummar Jiharsa Kan Abinda Ya Faru

Gwamnan PDP da Kujerarsa Ke Tangal-Tangal Ya Nemi Afuwar Al'ummar Jiharsa Kan Abinda Ya Faru

  • Gwamna Similanayi Fubara ya roki afuwar mazaunan jihar Ribas bisa rikicin siyasar da ya ɓarke a jihar a baya-bayan nan
  • Ya kuma bayyana abin da ya kai shi majalisar dokokin jihar Ribas da kuma yadda aka yi yunkurin tsige shi daga mulki
  • Fubara ya miƙa godiya ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda a cewarsa shiga tsakanin da ya yi ka iya warware matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya nemi afuwar al’ummar jihar kan rikicin siyasar da ya barke a jihar a baya-bayan nan, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Similanayi Fubara na jihar Ribas.
Gwamna Fubara Ya Nemi Afuwar Al'umma Kan Rikicin Da Ya Balle a Jihar Ribas Hoto: Sir Similanayi Fubara
Asali: Facebook

Ya bayyana rikicin a matsayin "Abin nadama da damuwa na 'yan kwanakin da suka gabata," yana mai cewa yana da mahimmanci a yi sadaukarwa don zaman lafiya ya ɗore.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Cikakken jerin gwamnonin Najeriya da ke da shahararrun iyayen gida a siyasa

Fubara ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya sa hannu mai taken, ‘Zaman lafiya ba shi da farashi’, wadda aka rabawa manema labarai ranar Asabar a Fatakwal, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tsokaci kan abin da ya faru, Gwamnan ya ce ya ziyarci zauren majalisar dokoki ne domin ganin ɓarnar da gobara ta yi da kuma ɗaukar matakin kare rayuka da dukiyoyi a majalisar.

A cewarsa, jim kaɗan bayan haka ya samu labarin majalisar ta dare gida biyu har an tsige shugaban masu rinjaye da wasu mutum uku kuma an fara yunkurin tsige shi daga gwamna.

A ɗaya ɓangaren kuma, ƴan majalisar suka tsige kakakin majalisa da mataimakinsa, lamarin da a cewar Fubara ya tada yamutsi a siyasar jihar Ribas.

Gwamnan ya nemi afuwar al'umma

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a sanarwan, gwamna Fubara ya ce:

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin gwamnonin da suka yi nasara kan iyayen gidansu na siyasa

“Ina tabbatar wa al’ummar jihar Ribas cewa lallai zaman lafiya da kwanciyar hankali zai wanzu kuma za mu ci gaba da hada kai domin ciyar da jihar mu gaba cikin lumana da tsaro.”
“A matsayina na gwamna, ina mai bai wa al’ummar jihar Ribas hakuri bisa yanayin damuwa da nadamar da suka shiga a ƴan kwanakin baya."

Ya kuma gode wa shugaban kasa, Bola Tinubu, kan shiga tsakani da ya yi wanda hakan ya buɗe hanyoyin da ka iya kaiwa ga warware rikicin cikin lumana.

Wasu illolin da yan bindiga suka yi a Katsina

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana wasu daga cikin illolin da matsalar tsaro ta haifar a rayuwar al'ummar jihar.

Ta ce sama da makarantu 120 aka rufe yayin da asibitioci 58 suka daina aiki a faɗin jihar duk sanadin ayyukan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel