Hatsarin Tirela da Adai-Daita Sahu Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8, 10 Sun Jikkata

Hatsarin Tirela da Adai-Daita Sahu Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8, 10 Sun Jikkata

  • Sakamakon hatsarin wata tirela da adai-daita sahu, mutane 8 sun mutu yayin da 10 suka jikkata a Mpape, Abuja
  • Sai dai ganin irin aika aikatar da yayi, direban tirelar ya tsere daga wajen, inda ya bar mutanen rai-a-hannun Allah, cikinsu har da dalibai guda biyu
  • Wasu na cewa burkin tirelar ne ya shanye amma wani ganau, ya shaidawa manema labarai cewa tayar motar ce ta fashe, wanda ya sa direban gaza shawo kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Akalla mutane takwas ne, cikinsu har da dalibai, wata mota kirar tirela dauke da yashi ta markade su har lahira sakamakon shanyewar burki a Mpape, wani kauye da ke kusa da gundumar Maitama, Abuja.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Hatsarin, kamar yadda rahotanni suka bayyana ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 4 na yamma, kafin a karasa garejin 'yan adai-daita sahu da ke kan titin da zai kai mutum zuwa ga sha-tale-talen Mpape.

Hatsarin mota
Akalla mutane 8 ne suka mutu a wani hatsarin tirela da adai-daita sahu a Abuja Hoto: DailyTrust
Asali: Twitter

Wani ganau, Mustapha Aminu, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa tirelar ta afkawa wasu mashinan adai-daita sahu da motoci, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 nan take, cikinsu har da dalibai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direban tirela ya tsere bayan ganin irin aika-aikar da yayi - Aminu

Aminu ya ce direban tirelar, ya shammaci mutane ya tsere ganin irin aika-aikar da yayi, inda ya bar motar a nan ya tsere da taimakon wani dan acaba.

"A lokacin da hatsarin ya faru. ina kusa da titin. Hatsarin ya yi munin gaske. Gawarwakin akalla mutane 8 ne aka kirga. Wasu na cewa burkin tirelar ne ya shanye. Amma a nawa ganin, tayar motar ce ta fashe, wanda ya yi sanadiyyar kwacewar motar daga hannun direban."

Kara karanta wannan

Matar aure ta nemi kotu ta datse igiyar aurenta bayan shekaru 2 babu haihuwa

"Babu wanda yaji ko da karar hon na tirelar, saboda sau tari idan irin wannan hatsarin ya faru, kana iya jiyo sautin hon na mota ko da kana daga nesa, hakan zaisa mutane su kaucewa titi. Da ace direban ya yi hakan, to da rayuka da dama basu salwanta ba."
"Akalla mashinan adai-daita sahu bakwai da wasu motoci hatsarin ya rutsa da su. Sannan akwai dalibai biyu a cikin ada-daita sahun, wadanda suka mutu nan take."

- Mustapha Aminu

Da yake tabbatar da faruwar hatsarin, kwamandan hukumar FRSC na Abuja, Chorrie Mutaa, yace jami'an hukumar sun ciro gawarwaki biyar da kuma mutane 10 da suka jikkata daga hatsarin.

Ya kara da cewa ababen hawa 13 ne hatsarin ya rutsa da su, ciki har da tirelar da ta haddasa hatsarin, sai adai-daita sahu da wasu motoci.

Ko a jihar Kwara irin wannan hatsarin ya taba faruwa, inda wata tirela ta makarde mutane 8 a Ilorin, babban birnin jihar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Tirela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah

Mutane takwas da wani adadin shanu da ba a fayyace bane suka mutu bayan wani tirela da ke tahowa daga arewacin Najeriya ya kutsa cikin wani mota da ake tsaye a Jihar Kwara.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne kusa da mahadar Okoolowo, karamar hukumar Ilorin Ta Kudu na jihar misalin karfe 6 na safen ranar Laraba kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel