Hatsarin mota ya hallaka mutane 15, wasu 42 sun jikkata

Hatsarin mota ya hallaka mutane 15, wasu 42 sun jikkata

An tabbatar da rasuwar mutane 15 sakamakon hatsarin da ya faru a yayin da wata trela dauke da shanu da kife a dalilin mugun gudu da ta ke yi a hanyar Minna zuwa Bida.

Wasu mutane 42 sun jikkata yayin da wata trela daban mai dauke da tumatur da barkono ta kife a hanyar Bida zuwa Mokwa.

Hukumar bayar da agaji na gaggawa na jihar Neja, NSEMA ta ce hatsarin biyu sun faru ne a ranar Lahadi.

An ajiye gawarwakin wadanda suka rasu a cibiyar lafiya ta gwamnatin taraya da ke Bida.

DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Hatsarin mota ya hallaka mutane 15, wasu 42 sun jikkata

Hatsarin mota ya hallaka mutane 15, wasu 42 sun jikkata
Source: UGC

Baya ga mugun gudu, babu wata dalili da ke tunanin shine ya haifar da hatsarin wadda ya salwantar da rayyuka 15 ciki har da direban motar.

Shugaban fanin kula da lafiya na FMC Bida, Dr Adedeji Olugbenga Adekanye ya tabbatar da rasuwar mutane 10 da aka kai gawarwakin su asibitin daga wurin da hatsarin ya faru.

Sai dai ya ce babu wanda ya bashi wani bayani bisa yadda hatsarin ya faru.

Adekanye ya kara da cewa an ajiye gawarwakin mutanen da suka rasu a dakin ajiye gawa na asibitin.

Wasu biyar da aka kawo su da ransu sun mutu sakamakon raunukan da suka ji.

Hatsarin ya biyu inda mutane 42 suka jikkata ya faru ne a lokacin da motar da kubcewa direban a yayin da ya ke kokarin shiga wata kwana a garin Gbadafu bayan an wuce garin Bida.

Trelan da aka cika da kaya da mutane da kayayakin abinci ya kife a yayin da direban ke kokarin shawo kan motar.

A yayin da ya ke magana da manema labarai a Minna, Shugaban NSEMA, Alhaji Ahmed Ibrahim Inga ya tabbatar da afkuwar hatsarin inda ya ce fasinjojin sun fito ne daga jihohin Katsina da Zamfara.

Shugaban na NSEMA ya ce hukumar tuni ta tuntubi iyalan wasu daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel