Tirela ta murƙushe ɗan kabu-kabu a jihar Abia

Tirela ta murƙushe ɗan kabu-kabu a jihar Abia

A ranar larabar da ta gabata ne, wata motar tirela maƙire da buhunan siminti, ta murƙushe wani direban kabu-kabu mai ƙafufuwa uku akan hanyar Mission ta birnin Umuahia a jihar Abia.

A bayanin wani mashaidin wannan hatsari da ya bayar da sunansa da Ikechukwu, mamacin ya rigamu gidan gaskiya ne a yayin da tirelar ta yi masa muguwar bangaza bayan yayi yukurin kauce mata.

Ma'aikatan FRSC

Ma'aikatan FRSC

Ikechukwu ya ci gaba da cewa, "tsautsayi dai baya wuce ranarsa amma ko shakka babu akwai ganganci da yayi sanadiyar wannan hatsari."

KARANTA KUMA: Rikicin makiyaya: Sarkin musulmi ya caccaki gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, jami'an hukumar kula da hanyoyi na FRSC sun dirfafa a wannan wuri bayan da lamarin ya afku, inda suka miƙa gawar direban zuwa ma'ajiyar gawarwaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel