Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Datse Igiyar Aurenta Bayan Shekaru 2 Babu Haihuwa

Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Datse Igiyar Aurenta Bayan Shekaru 2 Babu Haihuwa

  • Wata matar aure a Ilorin, ta roki kotu ta raba auren da ke tsakaninta da mijinta, saboda babu sauran wata soyayya a tsakaninsu
  • Matar ta kuma shaida wa kotun cewa, tsawon shekaru 2 ba ta yi ko da batan wata ba, don haka ta gaji da auren gaba daya
  • Sai dai mijin nata, ya tabbatar wa kotun cewa duk da Allah bai basu karuwa ba, yana son matarsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Wata matar aure, Shakirat Ayinla a ranar Alhamis, ta roki kotun kwastomare da ke da zama a Centre-Igboro Ilorin, jihar Kwara, ta datse igiyar aurenta, bisa dalilin da ta bayar na cewar ita da mijin sun kwashe shekaru biyu ba tare da haihuwa ba.

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood Hadiza Gabon Ta Maka Wani Mutum a Kotu Kan Bata Mata Suna

Mrs Ayinla ta shaida wa kotun cewa, a yanzu babu sauran wata soyayya a tsakanta da mijinta, Jimoh, kamar yadda rahoton Daily Nigerian ya nuna.

"Na riga da na yanke shawara kan wannan lamari tuntuni. Ina bukatar a datse igiyar auren nan," ta shaida wa kotun.

Kotun Kwastomari
Mrs Ayinla ta bukaci kotu ta datse giyar aurenta da mijinta, saboda rashin haihuwa Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke mayar da martani, Mr Jimoh, ya shaida wa kotun cewa, yana kaunar matarsa duk da cewa har yanzu Allah bai basu karuwa ba.

Sulhu bai yi wu ba tsakanin mu, in ji Mista Jimoh

Mista Jimoh ya shaida wa kotun cewa:

"Muna rayuwarmu cikin farin ciki, har sai a cikin watan Yuli, lokacin da ta bukaci zuwa Arewa, domin ziyartar 'yar uwarta, bayan da ta samu matsala a kasuwancinta.
Na amince da bukatarta. Har kudin abinci nakan aika mata lokaci zuwa lokaci. Amma na kadu matuka, lokacin da na samu labarin cewa ta dawo Ilorin, kawai dai ta ki dawowa gida ne."

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Ya cigaba da cewa:

"Na kirata domin jin ta bakinta, amma ta karyata hakan. Sai daga baya kuma ta amsa cewa makonni hudu kenan da dawowarta, ba ta dawo gida bane saboda ta gaji da zaman auren.
Na yi juyin duniyar nan, don mu sasanta ta dawo dakinta, amma ta kekashe kasa, akan ta gaji da wannan zaman, babu haihuwa."

Hukuncin da kotu ta yanke kan zaman auren Jimoh da matarsa

Mai shari'a, Abdulkadir Ahmed, ya ce kotun za ta so ace ma'auratan sun zauna sun sasanta wannan lamari tsakanin su.

:Kotu ba za ta iya tilasta kowanne bangare ci gaba da zaman aure ba."

- a cewar alkalin.

Da wannan ne kuma Ahmed, ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamba, domin ci gaba da sauraron karar.

Na daina kaunarsa a raba aurenmu, wata mata ta roki kotu

A ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, 2019, wata matar aure Aishatu Mohammed, ta roki kotun shari'ar musulunci da ke garin Minna, babban birnin jihar Niger, akan ba ta son mijin nata ko kadan yanzu, don haka kotun ta raba auren da ke tsakanin su, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Budurwa ta cire kunya ta nemi saurayi ya bata lamba, sun kusa aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel