Tirelar Da Jami’an Kwastam Su Ka Biyo Ta Afka Wa Wata Mata Da Yaranta 3

Tirelar Da Jami’an Kwastam Su Ka Biyo Ta Afka Wa Wata Mata Da Yaranta 3

  • Wata tirela da ake zargin jami’an hukumar kwastom, NCS ne su ka biyo a jihar Kwara ta afka wa wata mata da yaranta guda uku
  • Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a babban birnin jihar, Ilorin, kuma jami’an sun zargi tirelar cike take da shinkafar sumogal
  • Wannan lamarin ya auku ne bayan wata daya da jami’an su ka ci karo da wasu matasa a jihar yayin bin wata tirelar ta daban

Kwara - Jami’an hukumar kwastam, NCS, a jihar sun biyo wata tirela wacce ta fada wa wata mata da yaranta uku a ranar Talata da dare cikin Ilorin, Daily Trust ta ruwaito.

Mummunan lamarin ya auku ne bayan wata daya da jami’an kwastam din su ka ci karo da wasu matasa a Ilorin yayin da su ke kokarin kama wata tirela wacce take cike da kayan fasa kwauri.

Kara karanta wannan

An Bindige Jami'in FRSC Har Lahira A Kofar Gidan Abokinsa

Kwantena Ta Faɗa Kan Wata Mata Da Yara 3 Yayin Da Kwastam Ke Bin Trela a Kwara
Kwantena Ta Faɗa Kan Wata Mata Da Yara 3 Yayin Da Kwastam Ke Bin Trela. Hoto: LIB
Asali: Facebook

An samu bayanai akan yadda lamarin ya auku a daidai randabawul din garejin Offa kuma hakan ya yi sanadin cunkoso akan titin wanda aka kwashe sa’o’i ana yi.

Matasa sun bukaci a rufe hukumar kwastom din

Akwai fusatattun matasan yankin da su ka hau hayaniya su na bukatar a rufe hukumar, amma Daily Trust ta bayyana yadda ‘yan sanda su ka fatattake su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da dai babu asarar rayuka amma ganau sun sanar da City News cewa wata mata wacce take tuka mota kirar Mitsubishi ce ta ji mummunan rauni tare da yaronta daya cikin su ukun da abin ya ritsa.

Wakilin Daily Trust ya gano yadda yanzu hakan matar da danta su ke asibiti su na jinya, sai dai ba a bayyana sunan asibitin ba.

Da misalin karfe 9pm lamarin ya auku

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Wani ganau ya shaida cewa:

“Lamarin ya faru ne da misalin 9pm. Inda kwantenar tirelar ta fada wa matar da yaranta uku wanda hakan ya kwashe mintuna da dama.
“Jami’an kwastom din sun biyo tirelar ne wacce suke zargin cike take makil da shinkafar sumogal. Amma bayan ta fadi an gano itace ne a cikinta.”

Kakakin hukumar ya musanta bin direban

Kakakin hukumar kwastam na jihar, Chado Zakari, ya musa batun jami’ansu ne su ka biyo direban.

Kamar yadda ya shaida:

“Kawai sun gan mu ne a lokacin. Amma ba bin direban tirelar mu ka yi ba. Direban ya tsere kuma na tabbata da binshi mu ka yi a lokacin, da ya gayyaci abokansa don su yi mana aika-aika."

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Kara karanta wannan

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel