Abun Bakin Ciki: Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Kasa da Awanni 24 Bayan Mutuwar Mijinta

Abun Bakin Ciki: Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Kasa da Awanni 24 Bayan Mutuwar Mijinta

  • Allah ya albarkaci wata mata da haihuwar tagwaye kwana daya ta rasa mijinta
  • A wani bidiyon TikTok mai tsuma zuciya, an gano matar zaune a gadon asibiti tare da kyawawan yaranta
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka ga bidiyon sun ce zuciyarsu ta karaya sannan sun roki Allah ya tallafawa matar

Allah ya albarkaci wata matar aure da ta rasa mijinta da haihuwar tagwaye kasa da awanni 24 bayan mutuwarsa.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an tattaro cewa mutumin ya amsa kiran mahaliccinsa kuma bai samu damar yin arba da yaran nasa ba.

Ta haifi tagwaye awanni bayan mutuwar mijinta
Abun Bakin Ciki: Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Kasa da Awanni 24 Bayan Mutuwar Mijinta Hoto: TikTok/@mikepetersirkal.
Asali: TikTok

Bidiyon ya nuno matar zaune a kan gadon asibiti yayin da aka kwantar da tagwayen a gefenta. Alamu sun nuna ta haihu bai dade ba aka dauki bidiyon mai tsuma rai.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya siya wayar iPhone 15 amma ya tarar da teba a kwalin, ya koka a bidiyo

Mike Peters, wanda ya wallafa bidiyon ya roki Allah ya jagoranci matar wajen tayar da wadannan yara a bayan idon mahaifinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta a TikTok:

"Ta rasa mijinta a jiya sannan ta haifi tagwaye a safiyar yau. Allah ya taimake ta."

Mutane da dama da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa zuciyarsu ta kara sannan sun roki Allah da ya bai wa matar karfin tayar da wadannan yara.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan TikTok sun taya matar da ta rasa mijinta alhini

@user7679194470296 ya ce:

"Sylvia tamu. Allah na tare da ke, uwa."

@Essie ya ce:

"Ya ke Sylvia. Allah zai make ki kan wannan. Allah ya ji kan Guma da rahama."

@user8220814720728 ya ce:

"Wadannan yaran biyu rahama ne daga Allah. Mun ga aikin Allah a kanku ku uku. Ki kasance mai karfin zuciya. Akwai Allah."

Kara karanta wannan

Bidiyon jami’ar yar sanda tana rera taken kasa cike da kura-kuraiya girgiza intanet

@Mworeh ta ce:

"Allah ya sada ki da mala'ikun rahama su zagaye ki. Wadannan yara za su kawo farin ciki a gare ki."

Matashi ya tarar da teba a kwalin iPhone

A wani labari na daban, wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya wanda ke nuna wani mutum cike da nadamar zuwa siyan wayar iPhone 15 a kasuwar 'Computer Village.

Bayan ya siya wayar iPhone, ya bude kwalin kawai sai ya ga teba nade a cikin kwalin don sa shi ya yi nauyi kamar da gaske akwai abu a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel