Jami'an Tsaro Sun Fafata da Kasurgumin Dan Ta'adda a Jihar Neja

Jami'an Tsaro Sun Fafata da Kasurgumin Dan Ta'adda a Jihar Neja

  • Jami'an tsaro sun yi artabu da wani ƙasurgumin ɗan ta'adda a birnin Minna na jihar Neja, wanda ake zargin ɗan Boko Haram ne
  • Ɗan ta'addan wanda ya yi artabu da jami'an tsaron a gidansa ya tsere amma an cafke matarsa da ƴaƴansa
  • Jami'an tsaro sun ƙwato manyan makamai masu tarin yawa daga gidan ɗan ta'addan bayan sun gama gumurzu

Jihar Neja - An samu tashin hankali a birnin Minna, babban birnin jihar Neja, lokacin da wani da ake zargin ɗan kungiyar Boko Haram ne ya yi artabu da jami'an tsaro a daren ranar Talata, 23 ga watan Oktoba.

Jami'an tsaron dai sun kai samame ne a Unguwar Gebganu da ke Minna, inda gidan wanda ake zargin yake.

Jami'an tsaro sun fafata da dan ta'adda a Minna
Jami'an tsaro sun yi musayar wuta da dan ta'adda a Minna Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an gano aƙalla bindigu AK47 guda 150, harsasai kusan 3,000, bama-bamai, makamin roka da kuma bindigar harbo jirgi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Ga Ta Kansu Yayin da Jami'an Tsaro Suka Kutsa Cikin Daji, An Samu Babbar Nasara a Arewa

Rahotanni sun bayyana cewa harsashi ya samu wani mai gadi, Mubarak Abubakar, wanda ke gadi a wani gida kusa da gidan ɗan ta'addan, kuma yana samun kulawa a asibitin kwararru na IBB da ke Minna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kwashi tsawom lokaci ana fafatawa

Mazauna unguwar sun ce musayar wutar da aka fara da misalin karfe 12:00 na dare ya ɗauki tsawon sa'o'i da dama yayin da wanda ake zargin ya yi artabu da jami’an tsaro da muggan makamai kafin daga bisani ya tsere.

An bayyana cewa ya yi amfani da makamin roka ne ya rusa wani ɓangare na katangar gidansa inda ya tsere ta wajen, amma jami'an tsaro sun kama matarsa ​​da ƴaƴansa, rahoton Aminiya ya tabbatar.

An bayyana cewa wanda ake zargin ya fara harbe-harbe ne a lokacin da ya lura da isowar jami'an tsaro ta kyamarar CCTV da ya saka a gidansa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Tsaro, Sun Buɗe Wa Motocin Matafiya Wuta a Arewa

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ƴan sanda da gwamnatin jihar ba su ce komai ba dangane da wannna samamen da aka kai gidan ɗan ta'addan.

Yan Bindiga Sun Kashe Limami

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari ana cikin Sallah a ƙauyen Sabon Layi da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Ƙaduna.

Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka limamin wani masallaci da wani mutum ɗaya tare da raunata wasu mutum biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel