Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauci da Direbobi Biyu a Titin Jihar Kaduna

Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauci da Direbobi Biyu a Titin Jihar Kaduna

  • Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'in tsaro mafarauci da wasu direbobi biyu a titin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
  • Wani mazaunin garin ya bayyana cewa kusan kullum sai an yi jana'iza ta waɗan da suka ɓata a yankin
  • Sai dai da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ya ce yana cikin wani taro ba zai iya cewa komai ba

Jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'in tawagar mafarauta da ke taimaka wa wajen tabbatar da tsaro, Bashir Unguwar Shekarau, a kan titin Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Bayan haka, gungun 'yan ta'adda sun halaka ƙarin wasu mutum biyu direbobi a kan titin na Birnin Gwari, Mustapha Adamu da Malam Muktar, wanda aka fi sani da Malam.

Harin yan bindiga a Kaduna.
Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauci da Direbobi Biyu a Titin Jihar Kaduna Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa mafaraucin ya rasa rayuwarsa ne ranar Laraba sa'ilin da 'yan bindigan suka bude musu wuta yayin sintiri a kan babban titin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Masallaci a Lokacin Sallah, Sun Kashe Liman a Jihar Kaduna

Direbobin guda biyu suna kan hanyar koma wa Birnin Gwari ne da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Asabar, lokacin da ‘yan bindigar suka bude wa motocinsu wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin Birnin Gwari kuma ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, Shehu Randagi, ya ce an harbi wani direban a ido, yanzu haka yana Asibiti.

Mutumin ya ce:

"Sun farmaki mafarautan mu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum daya ranar Laraba. Hakan ta faru kafin harin da aka kai ranar Asabar, wanda ya yi sanadin mutuwar direbobin motocin haya biyu a kan titin."

A cewarsa, sauran mutane ukun da suka jikkata, ciki har da direban da ya rasa idonsa, Auwal Stable, suna karbar magani a asibiti.

Kullum sai an yi jana'iza

Randagi ya kuma koka kan ƙaruwar hare-hare da asarar rayukan jama'a a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota da Ya Auku a Kan Babban Titi a Najeriya

Ya ce mazauna ƙauyuka suna gudanar sallar jana'iza kan mutanen da suka ɓata kusan kowace rana, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, ya ce yana wurin wani taro ba zai iya cewa komai kan lamarin ba.

Wani mazaunin Birnin Gwari a Kaduna, Abubakar Usman, ya shaida wa Legit Hausa cewa a zahirin gaskiya yankin na fama da matsalar tsaro fiye da yadda ake tunani.

"Abun fa ya wuce tunanin mai tunani, mu kaɗai muka san halin da muke ciki, a gaskiya ya kamata gwamna Uba Sani ya waiwaye mu, Birnin Gwari na cikin matsalar tsaro."

Haka nan wani magidanci da ya nemi a sakaya bayanansa ya faɗa mana cewa kullum sai an kashe rai a wannan yankin sai dai kawai a yi addu'ar Allah ya kawo ƙarshen wannan lamarin.

Kara karanta wannan

Harin Fashi a Bankuna: An Kashe DPO da Wasu 'Yan Sanda Uku a Jihar Arewa, Sabbin Bayanai Sun Fito

Al'ummar Jihar Zamfara Sun Rubuta Wasika Zuwa ga Tinubu

A wani rahoton kuma Wasu mazauna garuruwan mazaɓar Sanatan Zamfara ta arewa sun rubuta wasiƙa zuwa ga gwamna da shugaban ƙasa Tinubu.

Mutanen a karkashin kungiyarsu, sun ja hankalin cewa 'yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankunan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel