Amarya Ta Fusata Bayan Angonta Ya Tiki Rawa da Mahaifiyarta

Amarya Ta Fusata Bayan Angonta Ya Tiki Rawa da Mahaifiyarta

  • Wani faifan bidiyon bikin aure ya nuna lokacin da wani ango ya yi rawa da surukarsa a wajen bikin aurensa, kuma da alama amaryarsa ​​ba ta ji daɗin hakan ba
  • Da alama matar ta ji cewa mijinta ya yi watsi da ita saboda yadda ya manne da mahaifiyarta, yana riƙe da ƙugunta yayin da suke rawa
  • Amaryar ta tsaya tana ta kallonsu da alamar baƙin ciki bayyane a fuskarta kuma ta sunkuyar da kai a cikin bidiyon, wanda ya fara yaduwa a TikTok

Wata Amarya tayi shiru tana kallon mahaifiyarta tana rawa cikin nishadi da mijinta a lokacin ɗaurin aurensu.

A cikin faifan bidiyon da shafin Official Wife TV ya sanya a TikTok, angon ya riƙe ƙugun surukarsa yayin da suke ta tiƙar rawa a wajen taron.

Kara karanta wannan

"Rashin Iya Soyayya" Kotu Ta Raba Auren Shekaru 9 Tsakanin Balkisu da Imam Kan Abu 1 Rak

Ango ya tiki rawa da surikarsa
Amarya ba ta ji dadin rawar da ango ya yi da mahaifiyarta ba. Hoto: TikTok/@officialkingswife1tv
Asali: TikTok

Da alama amaryar ta ji cewa an mayar da ita saniyar ware, saboda ɓacin rai ya lullube fuskarta yayin da take kallon abin da ke faruwa.

Tabbas matar ta so ta yi rawa da mijinta, amma angon ya nuna yana jin daɗin da rawa da surukarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rawar da angon ya yi da surukarsa ta haifar da ce-ce-ku-ce

A wasu lokutan a cikin faifan bidiyon, amaryar ta riƙa sunkuyar da kanta ƙasa a wata alama da ke nuna cewa ba ta jin daɗin abin da ke faruwa.

Masu amfani da shafukan sada zumunta da suka ga bidiyon sun ce abin da angon ya yi bai dace ba.

Bidiyon ya yaɗu sosai a yanar gizo, inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu a kai.

Wane martani ƴan soshiyal midiya suka yi?

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jihar APC Ta Yi Magana Kan Batun Sake Fitar da Gwamna Mara Lafiya Kasar Waje Domin Jinya

Ga kaɗan daga ciki:

@richardyorm ya rubuta:

"Wannan auren yana cikin HADARI!!!"

@Tirimud3 Hemaa ya rubuta:

"Amaryar ba ta jin daɗi ko kaɗan."

@Mrs.Swann ta rubuta:

"Mahaifiyar amaryar ta ce, "Ba na son zaman lafiya, ina son matsaloli."

Budurwa Ta Kunyata Saurayinta a Bainar Jama'a

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta kunyata saurayin a ɓainar jama'a bayan ya nemi ta yarda ya aureta.

Budirwar ta bar saurayin durkushe kan gwiwoyinsa tare da zoɓen neman tayin aurenta, inda ta yi watsi da buƙatarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel