Wata Mata Ta Bayyana Gaskiya, Inda Ta Ce 4 Daga Cikin Yaranta 6 Fasto Ne Ubansu

Wata Mata Ta Bayyana Gaskiya, Inda Ta Ce 4 Daga Cikin Yaranta 6 Fasto Ne Ubansu

  • Wata mata a Najeriya ta bayyana gaskiyar irin cin amanar da ta yi wa mijinta yayin zaman aurensu
  • Ta ce hudu daga cikin yaranta na wani Fasto ne a cocinsu inda ta ce daya kuma na mai siyar da nama
  • Matar ta bayyana wannan abin mamaki ne a wani shiri na gidan rediyon Kokoro Alate wanda ta halarta tare da mijin

Matar aure a Najeriya ta tona asirin kanta inda ta ce ta dade ta na cin amanar mijinta.

Matar ta bayyana haka ne yayin hira da gidan radiyo Kokoro Alate wanda ta halarta tare da mijin nata, Legit ta tattaro.

Mata ta bayyana cewa Fastonsu ne uban Yaranta 4 daga cikin 6
Mata Ta Bayyana Gaskiyar Yadda Ta Ci Amanar Mijinta. Hoto: Kokoro Alate TV.
Asali: Facebook

Meye matar ta ce game da cin amanar?

Wani mai kare hakkin dan Adam Oloye T. D ya wallafa faifan bidiyon a shafin Twitter inda matar ke bayani.

Kara karanta wannan

Matashi Na Shirin Yin Wuff Da Dattijuwar Baturiya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olaye ya nuna kaduwarshi yadda matar ke bayyana cin amanar da ta yi tare da mamakin ta yaya hakan ta faru.

A cikin faifan bidiyon, matar ta tabbatar cewa hudu daga cikin 'ya'ya shida na Fasto ne a cocinsu.

Ta ce ɗa daya ne kawai na mijin nata inda ta ce dayan kuma mai siyar da nama ne ubanshi.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Meye mutane ke cewa kan matar?

Mutane da dama sun yi martani kan wannan bidiyo na matar:

@Accur887:

"Idan kun san yara nawa Fastoci da Malamai da masu magani ke da su ku yi mamaki."

@adejumosamuel14:

"Ya kamata ko wane gida su na gwanin halitta, saboda yadda mata ke cin amanar mazajensu, yawan yaran da ba su san iyayensu karuwa ya ke."

@TejumolaSegun:

Kara karanta wannan

"Ta Kwanta Da Maza 5": Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Budurwarsa Ta Ci Amanarsa Daga Tafiya Kasar Waje

"Ba za mu roki ubangiji ya musu wata duniya na mata zalla ba. Maza su je su yi amfani da su idan sun dauki ciki sun haihu a kai duniyar maza in kuma mace ce a kai duniyar mata.

@God_Is_The_Plug:

"Ya kamata majalisar Tarayya ta kafa dokar hukunta irin wadannan shaidanun mata."

Fasto ya shawarci Kiristoci su kara aure

A wani labarin, Wani Fasto a kasar Ghana ya shawarci maza Kiristoci da su kara aure don samun tsawon rai.

Faston ya ce a matsayinsa na Kirista yanzu haka matansa guda biyu ne inda ya ce ya na jin dadin rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel