Wata Matar Aure Ta Kona Dan Kishiyarta da Dutsen Guga a Baya Kan N200 a Jihar Kuros Riba

Wata Matar Aure Ta Kona Dan Kishiyarta da Dutsen Guga a Baya Kan N200 a Jihar Kuros Riba

  • Abin takaici yayin da wata matar aure ta kona dan kishiyarta da dutsen guga mai zafi kan Naira 200 a jihar Kuros Riba
  • Matar mai suna Mary Ita ta aikata hakan ne a karamar hukumar Calabar ta Kudu inda ta ce yaron ba ya jin magana
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce ba su da masaniya kan wannan lamari

Jihar Kuros Riba – Ana zargin wata matar aure da kona dan kishiyarta da dutsen guga kan Naira 200 kacal a jihar Kuros Riba.

Wacce ake zargin mai suna Mary Ita ta aikata hakan ne a karamar hukumar Calabar ta Kudu da ke jihar.

Mata ta kona dan kishiyarta da dutsen guga kan satar Naira 200 a Kuros Riba
Wata Matar Aure Ta Kona Dan Kishiyarta da Dutsen Guga. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye dalilin kona yaron da matar ta yi?

Matar ta kona dan kishiyarta wanda aka ba ta goyo mai suna Daniel Offiong ta hanyar dodana masa dutsen gugan a gadon baya.

Kara karanta wannan

Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudi: Yadda Shagalin Bikin Wadda Ta Auri Kanta Da Kanta Ya Gudana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminiya ta tattaro cewa matar ta bayyana yaron da cewa kwata-kwata ba ya jin magana inda ya ke yawan dauke-dauken kudade da zarar an ajiye.

Ta ce a wannan karo ta ajiye makudan kudade amma sai da yaron ya lallaba ya zare har Naira 200 daga cikin kudaden.

Meye matar ta ce kan kona yaron?

Ta ce:

“Yaron ba ya jin magana ko kadan, duk lokacin da aka ajiye kudi sai ya sata saboda son kudi.
“Yanzu ma na kirga kudade na inda na fita amma kafin na dawo sai da ya lallaba ya zari Naira 200 a ciki.”

Mary ta ce dalilin hakan ne ma saboda ya bata mata rai ta dauki dutsen guga sai da ya yi zafi ta goga mishi a gadon baya, Paradise News ta tattaro.

Ta ce ta yi hakan ne don ya ji zafi kuma ya gane cewa aikata hakan kuskure ne da kuma rashin kyautawa.

Kara karanta wannan

Abin Takaici Yayin Da Mata Ta Yi Wa Mijinta Wanka da Tafasasshen Man Gyada, Mijin Ya Yi Bayani

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce ba su da masaniya kan wannan lamari har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sai dai Dakta Helen Isamoh, kwamishiniyar walwalar jama’a ta yi alkawarin ziyartar gidan don ganin halin da ake ciki.

‘Yan sanda sun kama matar da ta kona mijinta a Ribas

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda ta cafke matar da ta kona mijinta da tafasasshen ruwan zafi a jihar Ribas.

Matar mai suna Nwala ta kona mijin nata ne bayan ‘yar wata hatsaniya da ta faru a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel