Fusatacciyar Mata Ta Jika Gadon Kwanciyarsu Da Ruwa Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashi Yar Kanti

Fusatacciyar Mata Ta Jika Gadon Kwanciyarsu Da Ruwa Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashi Yar Kanti

  • Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno lokacin da wata matar aure ke zuba ruwa a kan gadon kwanciyarsu
  • Matar wacce ta fusata ta kwarara ruwa a gadon bayan mijinta ya ki siya mata gashi yar kanti mai tsada
  • Lamarin ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya game da rikicin ma'aurata da kuma tasirinsa a kan harkokin iyali

Wata matar aure yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nuna fushinta ga mijinta a wani yanayi da bai dace ba.

A wani bidiyo da @mufasatundeednut ya wallafa a Instagram, an gano matar tana zuba ruwa a kan gadonsu na sunna don nuna rashin jin dadinta kan abun da mijinta ya yi na ki siya mata gashi yar kanti mai tsada.

Matar aure tana jika gado
Fusatacciyar Mata Ta Jika Gadon Kwanciyarsu Da Ruwa Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashi Yar Kanti Hoto: @mufasatundeednut/Instagram.
Asali: Instagram
"Ba abu da yawa na nema ba. Sa'annina suna amfani da gashin kanti mai tsada" ta fada ma mijinta a kokarinta na kare kanta kan abun da ta yi.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Ruwa Yana Cikin Bacci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Wannan al'amari ya afku ne a gaban yaransu, wadanda suka cika da mamaki tare da takewa mahaifiyarsu burki kan abun da ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miji ya tsere zuwa otel bayan matarsa ta jika gadonsu da ruwa saboda gashi yar kanti

Sakamakon abun da ya afku a gidan, mijin ya dauki matakin kauracewa gidan ta hanyar kwana a otel, a kokarinsa na ganin lamarin bai ta'azzara ba.

Wannan abu da ya yi ya nuna soyayyarsu ta samu tangarda da kuma bukatar bayar da dan tazara domin kada lamarin ya munana.

Jama'a sun yi martani ga bidiyon matar da ta jika gadonsu

Nan take bidiyon ya yadu a dandalin soshiyal midiya, wanda ya haddasa cece-kuce game da yadda mutane ke nuna fushinsu da kuma tasirin irin wannan abu a harkokin iyali.

@derabliz ta yi martani:

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Gargadi Yan Mata Da Kyale Saurayinta Da Ya Siya Mota Kwanan Nan, Bidiyon Ya Ta Da Kura

"Mata yan uwanta sun mayar da hankali wajen aiki tukuru ita tana nan tana neman mai siya mata gashin kanti."

@nysc_catalogue ta ce:

"Bata da lafiyar kwakwalwa tana bukatar taimako."

@eldoradomedia ya ce:

"Idan kika takura mun, zan fece!"

@soft_hairmpire ta ce:

"Lallai matar nan ta ci karo da hira inda mijinta ya siyawa budurwarsa gashi yar kanti saboda wani irin hali ne wannan."

Matar aure ta fusata, ta kwararawa mijinta ruwa yana tsaka da bacci

A wani labarin kuma, wani bidiyo na wata matar aure da ke kwararawa mijinta da ke bacci ruwa ya haifar da zazzafan martani a soshiyal midiya.

Bidiyon wanda @SanphuSA ya wallafa a dandalin X ya yi fice, inda mutane da dama suka yi Allah wadai da abun da matar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel