“Masu Dukan Mazaje”: Mata 340 Ne Suka Lakadawa Mazajensu Mugun Duka a Lagas

“Masu Dukan Mazaje”: Mata 340 Ne Suka Lakadawa Mazajensu Mugun Duka a Lagas

  • Gwamnatin jihar Lagas ta samu rahotannin 340 na mata da ke dukan mazajensu tsakanin Satumban 2022 da Yulin 2023
  • Titilola Vivour-Adeniyi, shugabar hukumar yaki da cin zarafin mutane ta jihar, ta ce hakan na nuna maza sun fara barin dabiar yin shiru
  • Ta kuma ce alkaluma sun nuna cewa kaso 86.3 cikin dari na rahotannin cin zarafi da aka samu a kan mata ne

Jihar Lagos - Gwamnatin jihar Lagas ta ce akwai karin rahotanni 340 na mata masu lakadawa mazajensu mugun duka a cikin shekara daya da ta gabata, Satumban 2022 da Yulin 2023.

Titilola Vivour-Adeniyi, shugabar hukumar yaki da cin zarafin mutane ta jihar Lagas, ce ta bayyana haka, jaridar PM News ta rahoto.

An samu karuwar mata masu dukan miji a Lagas
An yi amfani da hotunan don kwatance ne Hoto: Benson Ibeabuchi/Bloomberg, Adekunle Ajayi/NurPhoto (Photos used for illustration)
Asali: Getty Images

A cewar shugabar hukumar ta DSVA, yawan maza da ke kai karar cin zarafin da ake masu ya karu cikin shekara daya da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Amince Da Sakin Biliyan 4.8 Don Gudanar Da Ayyuka Daban-Daban a Jihar Kano

Mata da ke dukan mazajensu: An kai rahoto 140 a shekarar da ta gabata

Vivour-Adeniyi ta ce adadin rahotannin guda 340 sun ninka adadin da aka samu tsakanin Satumba 2021 da Yuli 2022, wanda ya ke kan 140.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan alama ce ta cewar dabi'ar yin shiru a tsakanin jinsin maza dangane da batun cin zarafi ya fara raguwa," inji ta.

Cin zarafi: Mata sun fi shiga hatsari

Da take karin haske kan lamarin, Vivour-Adeniyi ta ce kashi 86.3 cikin dari na duk rahotannin da hukumar ta samu ana aikata su ne akan mata.

Ta bayyana cewa wannan ya cigaba ya kara karfafa sakamakon binciken da aka yi a baya cewa jinsin mata sun fi kasancewa cikin hatsarin fuskantar cin zarafi.

An tsinci gawar dalibar jami'ar Najeriya da ta bata

A wani labari na daban, mun ji cewa an tsinci gawar wata dalibar jami'ar tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah.

Kara karanta wannan

Wike: Abokin Fadan Atiku Ya Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Shari'ar Zaben 2023

An ayyana batan Atanda, dalibar sashin kula da jinya wacce ke a mataki na biyu bayan ta fita zuwa aji don yin karatu a daren ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, magatakardar jami'ar, Mufutau Ibrahim,ya tabbatar da cewar an gano gawar dalibar, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel