Yadda Dattijo Ya Tsara Budurwa a Wayar Tarho, Ya Ce Zai Sadaukar Mata Da Komai Nasa

Yadda Dattijo Ya Tsara Budurwa a Wayar Tarho, Ya Ce Zai Sadaukar Mata Da Komai Nasa

  • Wani dattijo ya tabbatar da cewar har yanzu yana da kalamai da zantukan da zai iya sace zuciyar mace duk da shekarunsa
  • An gano magidancin yana tattaunawa da budurwar tasa don fallasa mata sirrin zuciyarsa da irin son da yake mata
  • Tuni bidiyon ya haddasa cece-kuce a tsakanin matasa a soshiyal midiya inda suka dungi mamakin yadda aka yi yake da dadin baki har yanzu

Bidiyon wani dattijo dan kasar Ghana yana tsara budurwarsa da kalamai masu dadi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

An gano dattijon yana kokarin shawo kan matashiyar a wayar tarho, tare da fada mata irin sadaukarwar da ya yi don tabbatar da son da yake yi mata.

Dattijo yana waya da budurwa a waya
Yadda Dattijo Ya Tsara Budurwa a Wayar Tarho, Ya Ce Zai Sadaukar Mata Da Komai Nasa Hoto: @SIKAOFFICIAL1 Asali: Twitter
Asali: UGC

A cikin bidiyon da @sikaofficial1 ya wallafa a dandalin X, an gano dattijon a wani wuri mai kama da gona ko wajen hakar ma'adinai.

Kara karanta wannan

“Na Saduda”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca, Bidiyon Ya Taba Zukata

Mutumin, wanda ya sakaya rigarsa a kafada kuma sanye da jan takalmi, yana ta nanatawa budurwar irin son da yake mata a waya da kuma irin sadaukarwar da ya yi mata a bangaren kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Wannan ne dalilin da yasa bana wasa da lamarinki. Don haka ina son sadaukarwa da ba ki kudi koda ban ci abinci ba. Idan mutum ya samu taro kwabo ya baki ba zai taba boye maki takardun kudi ba."

Yayin da yake magana da ita, wasu abokan aikinsa sun karfafa masa giwa sannan sun fada masa abun da ai sanar da matashiyar. Daga bisani sai ya bayar da wayar ga wani mutum wanda ya ce ubangidansa ne don ya yi magana da budurwar tasa.

Da farko ubangidan nasa ya zata matarsa ce, amma sai dattijon ya fada masa cewa budurwarsa ce. Hakan na nufin mutumin na da aure sannan yake soyayya da wata a gefe.

Kara karanta wannan

“Sai Kace Lema”: Yadda Matashiyar Budurwa Ta Girgiza Intanet Da Yanayin Kitsonta Mai Ban Mamaki

Jama'a sun yi martani

@TimPvges ta rubuta:

"Yana da karfin gwiwa fiye da."

@breezy_litt ya rubuta:

"Ba yau mutumin nan ya fara ba."

@AppiahJ21 ta ce:

"Yi tunanin tafiya da shi a matsayin uba, zan so shi da yin koyi da shi."

Uba ya fashe da kuka a wajen bikin diyarsa

A wani labarin, wani bidiyo mai tsuma zuciya da ke nuna wani uba dan Najeriya cikin hawaye a ranar auren diyarsa ya tsuma zukatan masu kallo da dama a soshiyal midiya.

Mahaifin ya kasance zaune kusa da diyar tasa, wacce ke sanye da rigar amare, yayin da matarsa wacce ta kasance uwar amaryar ke ta murmushin farin ciki a daya bangaren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng