“Wa Ya Aike Ni”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi a Bidiyo Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca

“Wa Ya Aike Ni”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi a Bidiyo Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca

  • Bayan ta rasa kudinta a dandalin caca, wata matashiya yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya domin nuna nadamarta
  • Matashiyar ta sharbi kuka cike da dacin rai yayin da ta yi danasanin abun da ta aikata sannan ta magantu a kan yadda abun ya zame mata jiki
  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon a soshiyal midiya inda mutane da dama suka yi mata ba'a

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna @di_vine, ta koka a soshiyal midiya bayan ta rasa kudinta a harkar caca.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano matashiyar tana kuka yayin da take yi wa kanta fada kan shiga harkar caca da ta yi.

Budurwa ta rasa kudinta a caca
“Wa Ya Aike Ni”: Budurwa Ta Sharbi Kuka Wiwi a Bidiyo Bayan An Ci Kudinta a Gidan Caca Hoto: @just_that_girl_divine
Asali: TikTok

Ta gargadi mutane a kan su guji harkar caca, cewa yana zamewa mutum jiki. Ta ce abun ya kusa sanya ta daukar rayuwarta.

Kara karanta wannan

"1 Ne Naka": Mata Ta Fadawa Miji Gaskiya Cewa 4 Daga Cikin Yaranta 6 Malamin Addini Ne Ubansu, Bidiyon Ya Yadu

"Bana tunanin na taba irin kukan da caca ya sa ni a rayuwata," ta rubuta a bidiyonta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, mutane da dama ba su tausayinta ba ko kadan maimakon haka ma, sai suka dungi sukarta.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da intanet sun yi mata ba'a

Y2J ya ce:

"Musamman idan wasa daya ya yanke shi bayan ka gama tsara yadda za ka kashe kudin."

Is_larry ya ce:

"Sai ki dunga daukar kanki bidiyo kina kuka idan bidiyon bai dauku ba fa za ki sake kuka."

Licerrrr ya ce:

"Na rasa miliyan 4 a safiyar nan. Ba zan saduda ba."

Bad Character19 ya ce:

"Na rasa kudaden da ya kamata na yi amfani da su wajen gina gida a caca...Kusan miliyan 42...A takaice....ina cikin bashin miliyan 45."

“Idan rabo ya rantse”: Matashi dan Najeriya ya buga caca da N10, ya lashe miliyan N2

Kara karanta wannan

“Sai Kace Lema”: Yadda Matashiyar Budurwa Ta Girgiza Intanet Da Yanayin Kitsonta Mai Ban Mamaki

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna @isthatUW a Twitter ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya wallafa takardar caca da ya buga, wanda ke nuna ya ci miliyan N2.

Abun da ya ba mutane mamaki shine cewa da N10 kacal ya buga wasanni fiye da 146,000. Sa'arsa ya sa mutane yi masa tambayoyi a sashinsa na sharhi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel