Ginin Coci Ya Rufta Da Wani Fasto Yayin Da Su Ke Addu'o'i A Jihar Benue

Ginin Coci Ya Rufta Da Wani Fasto Yayin Da Su Ke Addu'o'i A Jihar Benue

  • Ana cikin tashin hankali yayin da wani ginin coci ya ruguje a Makurdi babban birnin jihar Benue
  • Rushewar ginin ya yi ajalin wani Fasto yayin da ya ke gabatar da addu'o'i da wasu mutane uku
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa sauran mutanen guda uku sun tsira daga iftila'in da ya faru a safiyar yau Talata

Jihar Benue - Wani ginin coci ya hallaka babban Fasto yayin da ya ruguje a kansa a jihar Benue.

Cocin Dunamis wanda ke Mission Ward a cikin birnin Makurdi ya rushe ne a safiyar yau Talata 3 ga watan Oktoba.

Ginin coci ya ruguje kan wani Fasto tare da hallaka shi a Benue
Ginin Coci Ya Rufta Da Wani Fasto A Jihar Benue. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

Yaushe ginin cocin ya rushe da Fasto a Benue?

Channels TV ta tattaro cewa lamarin ya afku ne yayin da Faston da mabiya guda uku ke gudanar da addu'o'i a cikin cocin a safiyar yau.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Da Ke Jihar Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mutanen guda uku sun tsira daga iftila'in yayin da ba a tabbatar da dalilin faruwar rushewar ginin ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.

Wasu gidaje da kuma wayoyin samar da wutar lantarki sun samu matsala dalilin rugujewar ginin a birnin.

Meye martanin 'yan sanda kan mutuwar Faston a Benue?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Benue, Anene Sewuese Catherine ta bayyana cewa ba su da masaniya kan wannan lamari da ya faru.

Legit ta tattaro cewa jami'an 'yan sanda da ke yankin sun riga sun isa wurin da lamarin ya faru yayin da 'yan ba da agajin gaggawa ke kawo dauki.

Ana yawan samun rushewar gine-gine a Najeriya musamman a irin wannan lokaci na damuna wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.

Fasto ya shawarci maza su kara aure don samun tsawon rai

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

A wani labarin, wani Fasto mai suna Meshack Aboh ya bai wa mazaje shawara da su kara aure don samun tsawon rai a duniya.

Aboh ya bayyana haka ne a ranar 19 ga watan Agustan 2023 inda ya ce idan har mutum ya na son tsawon rai dole ya auri mata fiye da daya.

Ya ce shi kam a yanzu haka ma ba mata daya ce gare shi ba inda ya shawarci Kiristoci da su sauya tunani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel