Fasto Ayodele Ya Bayyana Dalilin Bishop David Oyedepo, Paul Enenche Na Goyon Bayan Peter Obi

Fasto Ayodele Ya Bayyana Dalilin Bishop David Oyedepo, Paul Enenche Na Goyon Bayan Peter Obi

  • Primate Elijah Ayodele ya ce ƴan Najeriya bai kamata su ga laifin Bishop David Oyedepo, fasto Paul Enenche, da sauran fastocin da suka goyi bayan Peter Obi
  • Babban faston ya bayyana cewa Oyedepo, Enenche da sauransu sun goyawa Peter Obi baya ne saboda suna son canji a ƙasar nan
  • Ya yi bayanin cewa Oyedepo da Enenche sun sha bamban da fastocin da suka ce ba za ayi rantsuwa ba a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana dalilin Bishop David Oyedepo, fasto Paul Enenche, da sauran fastoci na goyon bayan Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa.

Ayodele ya ce bai kamata ƴan Najeriya su ga laifin fastocin ba ko su kira su na bogi, saboda abinda suke so kawai shi ne a samu a sauyi a ƙasar nan.

Fasto Ayodele ya bayyana dalilin manyan fastoci na goyon bayan Peter Obi
Ayodele ya ce canji fastocin suke so a samu a kasa Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele/Bishop David Olaniyi Oyedepo/Dr Paul Enenche/Mr Peter Obi.
Asali: Facebook

A cewar rahoton Nigerian Tribune, babban faston ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin.

Ayodele ya bayyana fastocin basu bayar da wani wahayi ba amma sun yi furuci da addu'a domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Faston ya bayyana cewa kamata ya yi a ga laifin ƴan takarar jam'iyyun adawa saboda ƙin yin amfani huɗubar da aka yi musu domin su lashe zaɓen.

A kalamansa:

"Yakamata mutane su daina caccakar manyan fastocin da suka goyi bayan Peter Obi ya zama shugaban ƙasa. Bai kamata ku ga laifinsu ba saboda abinda kawai suke so shi ne canji."
"Wahala ta yi yawa a ƙasa sannan suna buƙatar canji. Basu bayar da wani wahayi ba, abinda kawai suka yi shi ne maganganu. Irin su Paul Enenche, Oyedepo, da sauransu basu bayar da wani wahayi ba domin Peter Obi."

"Abin dariya ne idan wani ya ce fastocin Najeriya sun ba shi kunya saboda ko waɗanda suka yi magana akan ƴan takarar adawa ba wanda ya saurare su."
"Na bayyana cewa Tinubu ya shirya yin nasara ko ta halin ƙaƙa sannan na gayawa Obi da Atiku abinda yakamata su yi su ci zaɓen, amma sun yi hakan? Meyasa kuke ganin laifin fastocin Najeriya."

Oyedepo, Enenche sun bambanta da fastocin da suka ce ba za ayi rantsuwa ba

Ayodele ya yi ƙarin haske kan cewa fastocin da ya lissafo sun bambanta da sauran fastocin da suka ce ba za a gudanar da rantsuwa ba a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.

"Bana magana ne akan fastocin da suka ce ba za ayi rantsuwa ba, ina magana ne akan waɗanda suka marawa Obi baya a lokacin zaɓe ta hanyar amfani da cocinsu." A cewarsa.

Primate Ayodele Ya Hango Wani Mummunan Abu Da Zai Faru a Mulkin Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, Primate Ayodele ya yo hangen wani abu mara kyau da zai faru a mulkin shugaba Bola Tinubu.

Babban faston ya bayyana cewa ci gaban wasu jihohi zai samu tawaya saboda rikicin da gwamnonin jihar za su riƙa yi da magabatansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel