Gwamnati Ta Shawo Kan Ma’aikata, Za a Iya Fasa Shiga Yajin-Aiki a Duk Najeriya

Gwamnati Ta Shawo Kan Ma’aikata, Za a Iya Fasa Shiga Yajin-Aiki a Duk Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ajiye magana da ‘yan kwadago saboda a fasa shiga yajin-aiki a makon nan
  • Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma ya fitar da jawabin matsayar da aka cin ma a taronsu
  • Sanarwar Mallam Mohammed Idris ta ce za a kai bukatun NLC da TUC zuwa wajen Bola Tinubu

Abuja - Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago sun cin ma yarjejeniya domin fasa yin yajin-aikin da aka yi niyya a duk fadin Najeriya.

Tribune ta ce an yi nasarar hakura da wannan yajin-aiki ne bayan dogon zaman da bangarorin biyu su ka yi a ranar Lahadi, 1 ga Oktoban 2023.

Sanarwar matsayar da aka cin ma ta na cikin jawabin bayan taron ‘yan kwadago da wakilan gwamnatin tarayya domin a iya gano bakin zaren.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Sanar Da Karin Albashi Ga Dukkan Ma’aikata Bayan Ganawar FG Da Kungiyar Kwadago

'Yan kwadago
'Yan kwadago su na son yin yajin-aiki Hoto: theconversation.com
Asali: UGC

Sai babu yajin-aiki za a sasanta

Ma’aikatan sun amince su fasa kauracewa wuraren ayyukansu ne ganin cewa zai fi sauki a shawo kan duk wasu sabani idan ba a tafi yaji ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mallam Mohammed Idris ya fitar da jawabi a daren Litinin bayan awa hudu ana zama a Abuja.

Rahoton ya ce Mallam Mohammed Idris ya nuna NLC da TUC za su yi la’akari da tayin da gwamnati tayi masu domin a fasa durkusa kasar.

Za a kai wa shugaban kasa bukata

Lura da haka kungiyoyin kwadago sun bukaci karin albashi, wanda bangaren gwamnati zai gabatar ga mai girma shugaba Bola Tinubu.

Gwamnati tayi alkwarin duba rikicin RTEAN da NURTWA a Legas a taron da ya samu halartar ministoci shida da NSA, Malam Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

"Tattakin Neman Yanci": Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa

Yunkurin da gwamnati ta ke yi

Saboda a ajiye maganar yajin-aiki gwamnati ta amince da karin albashi ga duka rukunin ma’aikata.

Bugu da kari, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta janye harajin VAT da ke kan dizil na tsawon watanni shida, hakan zai saukaka kasuwanci.

A daidai lokacin da ake kokawa da cire tallafin man fetur, gwamnati za ta kokarta wajen samar da motoci masu amfani da CNG a kasar nan.

A wata sanarwa, hadimin shugaban Najeriya ya ce za a biya iyalai miliyan 15 tallafin N75,000 na tsawon watanni uku na karshen shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel