TUC Ta Taso Shugaba Tinubu a Gaba, Ta Ce Dole Ya Bayyana Kudin da Ya Tara Daga Cire Tallafin Fetur

TUC Ta Taso Shugaba Tinubu a Gaba, Ta Ce Dole Ya Bayyana Kudin da Ya Tara Daga Cire Tallafin Fetur

  • Ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu na shan wahala a Najeriya bayan cire tallafin man fetur
  • Shugaban NLC ya bayyana bukatar gwamnati ta fadi yadda ta kashe kudin da ta tara daga cire tallafin mai
  • Legit Hausa ta tattauna da ma'aikacin gwamnatin tarayya, ya bayyana irin wahalar da yake sha a yanzu

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar kwadago kuma ta 'yan kasuwa Festus Osifo, ya bukaci gwamnatin tarayya ta fitar da lissafin kudaden da ta tattara tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayu.

A watan Yuli ne dai shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin Najeriya ta ceto sama da Naira tiriliyan daya daga cire tallafin man fetur, Ripples Nigeria ta ruwaito.

An nemi Tinubu ya bayyana kudin da ya tara daga cire tallafi
Bayan cire tallafi, TUC ta bankado Tinubu | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AriseTV a ranar Laraba, Osifo ya ce da irin wadannan makudan kudade a hannun gwamnati, shugaban kasar ba shi da wata bukatar cin bashi.

Kara karanta wannan

Kowa Ma Ya Rasa: Tsohon Shugaban FIRS Ya Lallaba Ya Kwashe Naira biliyan 11 Kwanaki 2 Bayan An Koreshi

Shugaban NLC ya yi magana

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Shugaban kasa ya fito ya ce kasar nan ta ceto Naira tiriliyan 1. Gwamnatin Tarayya ta je ko’ina ta sanar da cewa idan aka cire tallafin man fetur, za ta ceto makudan kudade.
“Saboda haka, ba ma tsammanin za su je waniw uri su fara rancen kudi. Sun ce mana za su tara kudi. To ina kudaden da kuka tara, kuma ta yaya suka kashe wadannan kudaden?”

Ma'aikatan gwamnati na shan wahala

Osifo ya koka da yadda galibin ma’aikatan gwamnati ke zama ko ma kwana a ofisoshinsu a ranakun aiki saboda tsadar hada-hada.

Ya bayyana cewa, mafita shine gwamnati ta bayyana meye ta yi da wadannan kudade tare da kawo sauki ga ma'aikata, Daily Nigerian ta tattaro.

Ya kuma bayyana cewa, hakan ya shafi ma'aikatan masana'antu masu zaman kansu a kasar nan.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

Yanzu ba ma sha'awar aikin gwamnati

M U Faruk Yunus, wani malamin jami'ar tarayya da ke Nasarawa ya bayyana cewa, yanzu aikin gwamnati ya zama aikin ban tausayi.

A cewarsa:

"A yanzu aikin gwamnati wahalarsa ta fi yawa. Matukar ahalinka na wani gari kuma kana aikin gwamnati a wani gari, masu mota kake tarawa kudi, sai dai kuma idan za ka yi watsi da ahalinka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel