Abubuwan Da Za Su Jawo Shinkafa, Sauran Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Bana - Dr Yusuf

Abubuwan Da Za Su Jawo Shinkafa, Sauran Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Bana - Dr Yusuf

  • Dr. Sanusi Muhammad Yusuf ya fada mana abubuwan da su ka bada gudumuwa wajen tashin kudin abinci
  • Masanin harkar gonan ya na ganin akwai tasirin rashin tsaro da cire hannun gwamnati da babban bankin kasa wato CBN
  • Buhun kayan abinci sun tashi saboda rashin tsaro a jihohin Arewacin Najeriya da wasu kasashen nahiyar Afrika

Dr. Sanusi Muhammad Yusuf malamin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria (ABU) ne kuma masani a harkokin dabbobi da kayan abinci, ya yi wata hira da Legit Hausa.

A tattaunawar da mu ka yi da shi, ya yi mana hasashen cewa kayan abinci za su cigaba da tsada a kakar bana saboda wasu dalilai.

Abinci
Wata gonar shinkafa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin gaskiya ne an fuskanci karancin kayan amfanin gona?

Akwai karancin kayan gaskiya, abubuwa barkatai su ka jawo hakan. Na farko akwai matsala domin a baya gwamnati ta na bada tallafi wajen noman damina – a noman bara babu tallafin takin zamani, ba a sabunta yarjejeniyar da gwamnatin Najeriya tayi da kasar Moroko ba. Farashin takin NPK da Urea da maganin feshi ya yi yawa, sai da Urea ta kai N26, 000 yayin da buhun NPK ya kai N28, 000. Sannan kwalin maganin feshi ya tashi, wannan ya jawo tsadar abinci. Sannan ba kowa ne ya iya yin noma ba saboda tsadar hatsi, sanadiyyar haka sai abin da mutane su ke nomawa ya ragu.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Fallasa Matsalar da Ta Hango Gabanin Zaben Gwamna a Jihohi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma rashin tsaro.

Ga kuma matsalar ‘yan bindiga da ya hana mutane shiga gonaki, duk wadannan sun rage adadin hatsin da ake samu a kasuwa. Baya ga haka, bankin CBN bai bada kudin noma ba saboda ana kokarin karbo bashin da aka bada. Gwamnati ba ta bada karfi wajen noman shinkafa a shekarar da ta wuce ba.
Na farko ba ayi noman da yawa ba, na biyu kuma an samu karuwar manya-manyan kamfanonin casar shinkafa. Alal misali mu na iya cashe metric tona 728, kuma ko a Kano akwai kamfanonin da su ka fi shi girma. Idan akwai manyan kamfanoni irin haka, za ayi wa samfarerar shinkafar da aka noma yawa.
Ana haka kuma sai gwamnatin tarayya ta sa dokar ta-baci a kan harkar abinci. Yanzu ma’aikatun gwamnati su na shiga ko ina domin nemo kayan abinci domin babu a rumbunan gwamnati. Huro wuta da aka yi ya taimaka wajen kawo tsada da karancin kayan abinci. Bugu da kari, akwai matsalar tsaro a kasashen Afrika irinsu Burkina Faso, Mali da Nijar da ta rufe iyakarta, duk abincin da za su fito daga Ghana, Togo da Benin ya taimaka wajen tashin farashi.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Gwamnan CBN Ya Sha Alwashin Dakile Tashin Farashin Kaya, Ya Fadi Dalillai

Buhunan abinci za su yi tsada kenan?

Duk wadannan abubuwa da na ambata za su cigaba da jawo tashin farashi. Idan ka duba daminan yanzu, an samu karancin ruwan da ya taba gonaki. Akwai wuraren da amfanin gona sun kone saboda rashin isasshen ruwan sama. Noman rani bai yi kyau ba kuma daminar ba ta zo da ruwa sosai ba. Tsadar iri ya bada gudumuwa wajen rage adadin abin da ake nomawa, baya ga rashin tsaro da ya addabi wasu yankuna har gobe.

Salon mulkin Bola Tinubu

Kun ji labari Shugaban Najeriya mai-ci watau Bola Tinubu ya nuna ya sha bam-bam da Muhammadu Buhari da ya damka masa mulki a Mayun bana.

Tinubu ya ce ba zai zama shugaban kasan da zai rika bada uzurori ba, zai tunkari matsalolin kasar, har yake cewa ‘yan Najeriya ba malalata ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel