Babban Basaraken Inyamurai a Jihar Oyo Ya Yi Bankwana Da Duniya

Babban Basaraken Inyamurai a Jihar Oyo Ya Yi Bankwana Da Duniya

  • An shiga jimami bayan an yi rashin babban basaraken Igbo (Eze Ndigbo) na Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Dr. Alex Anozie
  • Babban basaraken ya mutu ne a gidansa da ke Ososami cikin birnin Ibadan a ranar Talata, 26 ga watan Satumban 2023
  • Majiyoyi na kusa da basaraken sun tabbatar da cewa basaraken wanda ya yi bankwana da duniya yana da shekara 74, bai nuna alamun rashin lafiya ba

Jihar Oyo - Eze Ndigbo na Ibadan kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya waɗanda ba ƴan asalin Ibadan ba, a jihar Oyo, Alex Anozie, ya yi bankwana da duniya.

Basaraken wanda ya rasu a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, ya mutu yana da shekaru 74 a duniya.

Basaraken Inyamurai na Ibadan ya mutu
Dr Alex Anozie, ya mutu yana da shekara 74 a duniya Hoto: Eze Dr Alex Anozie
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa basaraken ya mutu ne a gidansa da ke Ososami cikin birnin Ibadan, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

Anozie ya fito ne daga Igboukwu, a cikin ƙaramar hukumar Aguata ta jihar Anambra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya basaraken ya bar duniya?

Ɗaya daga cikin na kusa da basaraken wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa marigayin bai nuna wata alamar rashin lafiya ba kafin mutuwarsa, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

A kalamansa:

"Marigayin ya yi rayuwarsa ne a Ibadan kuma ya bayar da gudunmawa sosai wajen bunƙasar tattalin arzikin birnin mai daɗaɗɗen tarihi. Ya rasu ne a ranar Talata a cikin gidansa na Ososami da ke a Ibadan, babban birnin jihar."
"An tafi da gawarsa zuwa asalin garinsu na Igboukwu dake ƙaramar hukumar Aguata ta jihar Anambra domin binne shi."

Kafin mutuwarsa, ya kasance Manajan Darakta kuma shugaban kamfanin CONAC Optical Company, da ke Ibadan.

Babban Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Delta ta yi rashin ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta da take ji da su.

Kara karanta wannan

Eid-el-Maulud: Gwamnan Jigawa Ya Ayyana Alhamis a Matsayin Ranar Hutu

Cif Charles Abude wanda ya taɓa yin takarar gwamna da sanata a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, ya faɗi ya mutu ne a ƙaramar hukumar Sapele ta jihar.

Obule, wanda yake riƙe da sarautar “Erhi na masarautar Okpe” ya mutu ne ya bar duniya yana da shekara 65 bayan ya daɗe yana fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel