Bikin Maulidi: Gwamnan Jigawa Ya Tsawaita Hutu Zuwa Ranar Alhamis

Bikin Maulidi: Gwamnan Jigawa Ya Tsawaita Hutu Zuwa Ranar Alhamis

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta tsawaita hutu har zuwa ranar Alhamis domin bikin maulidi na 2023
  • Ofishin shugaban ma'aikata ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba
  • Ku tuna cewa gwamnatin tarayya ta sanar da yau a matsayin hutu domin bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ayyana ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba a matsayin hutu domin bikin Maulidi na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, jami'in hulda da jama'a na ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba.

Gwamnan Jigawa ya ba da hutun Maulidi
Bikin Maulidi: Gwamnan Jigawa Ya Tsawaita Hutu Zuwa Ranar Alhamis Hoto: Jigawa State Radio
Asali: Facebook

PM News ta rahoto cewa shugaban ma'aikatan jihar, Muhammad Dagaceri, ya ce wannan yunkurin ya biyo bayan umurnin da Namadi ya bayar ne.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bada Hutun Ranar Haihuwar Manzon Allah SAW Bayan Wanda Gwamnatin Tinubu Ta Sanar

Sanarwar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na rubuto wannan takarda don sanar da cewa gwamnatin ta ayyana ranar 12 R/Awwal, 1445AH (28 ga watan Satumban 2023) a matsayin hutu domin bikin Haihuwar Annabi Muhammad S.A.W (Malud Nabiy)."

Dagaceri ya bukaci ma'aikata da daukacin al'ummar Musulmi a jihar da su zamo masu hakuri da addu'a don zaman lafiya, natsuwa, da cigaba.

Ya kuma bukaci mazauna jihar da su roki Allah ya kare da yi wa shugabanni jagoranci wajen jan ragamar harkokin jihar Jigawa da Najeriya baki daya.

Eid-el-Maulud: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutu

A baya mun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bayyana Laraba, 27 ga Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu domin bukuwan murnar zagayowar Maulidi na shekarar 1445H.

Wasu daga cikin mabiya addinin Musulunci musamman yan darika, qadiriya da sauransu suna bikin Maulidi ne don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Maulidi: Sakon Shugaba Tinubu Ga Al'ummar Musulmai Yayin Da Ake Shirin Bikin Maulidi

An ba da hutun ne a cikin wani jawabi daga babban Sakataren ma'aikatar cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade, a madadin Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

A sanarwan, Ministan cikin gida ya taya ɗaukacin al'ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar bukukuwan Maulidi na wannan shekarar.

Tinubu ya taya Musulmai murnar zagayowar haihuwar Annabi

A gefe guda, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su yi wa kasar addu'a da kuma gwamnatinsa.

Tinubu ya yi wannan rokon ne yayin taya al'ummar Musulmai murnar bikin Maulidi da za a yi gobe.yayin taya al'ummar Musulmai murnar bikin Maulidi da za a yi gobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel