Allah Ya Yi Wa Kanin AGF Malami Rasuwa Yana Da Shekaru 55

Allah Ya Yi Wa Kanin AGF Malami Rasuwa Yana Da Shekaru 55

  • Tsohon atoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, da ahlinsa sun riski kansu a yanayi na bakin ciki
  • Hakan ya kasance ne sakamakon rashi da suka yi na kanisa, Dr Khadi Zubairu Malami, wanda ya rasu yana da shekaru 55 a duniya
  • Marigayi Dr Zubairu Malami ya rasu a safiyar Litinin, 5 ga watan Yuni, bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke Birnin Kebbi

Allah ya yi wa kanin tsohon atoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, rasuwa.

Margayi Dr Khadi Zubairu Malami, ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Yuni bayan yar gajeruwar rashin lafiya a gidanda da ke Birnin Kebbi, jaridar Leadership ta rahoto.

Jama'a a wajen jana'izar kanin Malami
Allah Ya Yi Wa Kanin AGF Malami Rasuwa Yana Da Shekaru 55 Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Gwamnan Kebbi ya yi alhinin mutuwar kanin Malami

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Rahotanni sun kawo cewa Zubairu ya mutu ya bar matar aure daya da yara biyar kuma tuni aka binne shi daidai da koyarwar addinin Musulunci a Birnin Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nasir Idris Gwandu, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa gidan marigayin ya yi ta'aziyyar ga Malami da iyalan mamacin sannan ya roki Allah SWT ya yafe masa kurakuransa a nan duniya da lahira, jaridar The Sun ta rahoto.

Manyan masu fada aji da dama daga cikin jihar Kebbi da wajenta sun yi tururuwa zuwa gidan margayin domin yi wa tsohon AGF din da iyalan mamacin gaisuwan ta'aziyya.

Allah ya yi wa sarki mafi dadewa a Najeriya rasuwa bayan ya shafe shekaru 64 kan kujerar mulki

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Allah ya yiwa Joseph Davies-Agba, basaraken gargajiya na masarautar Obudu rasuwa.

Kara karanta wannan

Malamin Addini Ya Ci Gyaran Abba Gida-Gida, Ya Fadi Yadda Gwamna Zai Karbe Fili

Dan marigayi sarkin, Kjay Jedy-Agba ne ya sanar da labarin mutuwar mahaifinsa a ranar Lahadi a garin Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Marigayi sarkin gargajiyan, wanda ya shafe shekaru 64 a kan karagar mulki, ana bayyana shi a matsayin sarki mafi dadewa a kan karagar mulki a Najeriya.

Kamar yadda rahotannin suka kawo, Jedy-Agba ya ce za a sanar da jama'a cikakkun bayanai game da jana'izar marigayi sarkin da zarar an kammala bukukuwan gargajiya da na al'adu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel