Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yayanta a Jihar Kwara

Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yayanta a Jihar Kwara

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da wata mata da ƴaƴanta guda uku a wani sabon hari da suka kai a jihar Ƙwara
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne dai a ƙauyen Ajilete cikin gundumar Agunjin a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar
  • Majiyoyi daga ƙauyen sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka ce ƴan bindigan sun nemi a biya su N100m a matsayin kuɗin fansa

Jihar Kwara - Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da ƴaƴanta guda uku a ƙauyen Ajilete, gundumar Agunjin a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba, da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Yan bindiga sun sace mata da yayanta a jihar Kwara
Yan bindigan sun bukaci a biya su N100m a matsayin kudin fansa Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Har ya zuwa yanzu dai ba a tantance sunayen mutanen da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Ƙazamin Hari Jihar Kaduna, Sun Halaka Mutane da Yawa

An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun yi dirar mikiya ne a ƙauyen inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen daga cikin gidajensu zuwa cikin daji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na wa ƴan bindigan suka nema a matsayin kuɗin fansa?

Sai dai, wasu majiyoyi daga cikin mazauna ƙauyen sun ce masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan mutanen da suka sacen inda suka buƙaci a biya su naira miliyan 100.

Jaridar Daily Trust ta ce da yake magana kan batun a ranar Talata, shugaban kwamitin riƙon kwarya na ƙaramar hukumar, Jide Asonibare, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce babu wani ci gaba da aka samu kan lamarin.

A kalamansa:

"Tuni mun sanar da ƴan sanda da sojoji a jihar Kwara da makwabtanmu jihar Kogi. Ƴan banga 15 har yanzu suna cikin dajin suna nema, amma babu wani cigaba da aka samu."

Kara karanta wannan

Jerin Fastocin Da Suka Yi Hasashen Za a Cafke Peter Obi a Watan Satumba

"Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan mutanen da suka sace suna neman a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 100."

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kwara ba, Okasanmi Ajayi, domin bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba.

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai

A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun kai hari a kwalejin kimiyya da fasaha ta Mustapha Agwai I da ke a garin Lafia, jihar Nasarawa.

Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a kwalejin, sun harɓi ɗalibai gudu uku tare da yin garkuwa da wata ɗaliba guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel