Majalisa Ta Fara Tantance Yemi Cardoso Domin Zama Gwamnan CBN

Majalisa Ta Fara Tantance Yemi Cardoso Domin Zama Gwamnan CBN

  • Majalisar dattawan Najeriya ta fara tantance Yemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
  • Majalisar za ta kuma tantance mataimakan gwamnan bankin CBN guda huɗu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa
  • Idan majalisar ta amince da naɗin Yemi Cardoso da Shugaba Tinubu ya yi, zai zama wanda zai maye gurbin Godwin Emefiele a shugabancin CBN

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta fara aikin tantance Olayemi Cardoso, wanda aka naɗa a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)

Bugu da ƙari, majalisar dattijai tana kuma tantance sunayen mataimakan gwamna huɗu a babban bankin, cewar rahoton The Punch.

Majalisa ta fara tantance Yemi Cardoso
Shugaba Tinubu ya nada Cardoso a matsayin magajin Emefiele Hoto: Yemi Cardoso
Asali: Facebook

Wadanda aka naɗa mataimakan gwamnan na CBN sun haɗa da Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Philip Ikeazor, da Bala Bello.

An fara aikin tantancewar ne biyo bayan ƙudirin da Opeyemi Bamidele, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ya gabatar.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Hana Majalisa Tsige Mataimakin Gwamnan APC, Ta Bayyana Dalilanta

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cardoso da sauran mataimakan gwamnonin guda huɗu na CBN da aka naɗa sun samu rakiyar babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Gumel, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Cardoso ya fara aiki a CBN

A makon da ya gabata ne Cardoso ya fara aiki a matsayin muƙaddashin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) har zuwa lokacin da majalisar dattawa za ta tantance shi da amincewa da naɗin da shugaban ƙasa ya yi masa.

A ranar 15 ga watan Satumba ne Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Yemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Shugaba Tinubu ya kuma sanar da amincewarsa da naɗin mataimakan gwamnoni huɗu na CBN na tsawon shekaru biyar kowanne a matakin farko, har zuwa lokacin da majalisar dattawa ta amince da su.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Saka Ranar Tantance Gwamnan CBN, Mataimakansa Da Wasu Ministoci 2

Emefiele Ya Hakura Da Shugabancin CBN

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ɗauki dangana inda ya yi murabus daga shugabancin bankin na CBN.

Godwin Emefiele wanda ya kasance a tsare a hannun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) tun bayan dakatarwar da aka yi masa, ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne ga Shugaba Tinubu a cikim watan Agustan 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel