Godwin Emefiele Ya Yi Murabus Daga Shugabancin CBN

Godwin Emefiele Ya Yi Murabus Daga Shugabancin CBN

  • Godwin Emefiele wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar daga shugabancin babban bankin Najeriya (CBN), ya yi murabus
  • Emefiele ya yi murabus ne daga muƙamin gwamnan babban bankin a cikin watan Agustan 2023
  • Murabus ɗin na Emefiele ya kawar da duk wata matsala ta fannin shari'a kan naɗin Yemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN da Tinubu ya yi

FCT, Abuja - Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugabancin bankin.

Emefiele ya miƙa takardar yin murabus daga mukamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ne a watan Agustan 2023.

Emefiele ya yi murabus daga shugabancin CBN
Godwin Emefiele ya ba Shugaba Tinubu takardar murabus dinsa Hoto
Asali: UGC

A cewar rahoton Reuters, Emefiele wanda aka dakatar daga muƙaminsa a watan Yuni, ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

An fahimci cewa tun da farko ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), amma hukumar ta yi watsi da ita saboda doka shugaban ƙasa kawai ta ba shi hurumin miƙa wa takardar murabus ɗin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene abin da murabus ɗin Emefiele ke nufi?

Yin murabus ɗin na Emefiele, ya sanya an kawar da matsalolin shari'a game da naɗin Yemi Cardoso a matsayin sabon gwamnan CBN.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin watsa labarai, ya sanar da naɗin Cardoso.

Shugaban ya kuma naɗa sabbin mataimakan gwamnan CBN guda hudu wato, Emem Nnana Usoro, Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Philip Ikeazor da Bala M. Bello.

Idan majalisar dattawa ta amince da naɗin da shugaban ƙasar ya yi masa, ana sa ran Cardoso zai yi aiki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan CBN.

Binciken Emefiele Zai Tona Asirin Manya

A wani labarin na daban kuma, binciken da Shugaba Tinubu ya sanya a yi masa kan babban bankin Najeriya, zai jefa manya da yawa cikin matsala.

Jami’in da Bola Ahmed Tinubu ya kawo musamman domin ya yi bincike a kan ayyukan CBN ya shirya fara tasa keyar ma’aikatan bankin.

Jim Obazee zai fara tsare manyan jami’ai ya na yi masu tambayoyi kan zargin ba dai-dai ba da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel