Kotu Ta Hana Majalisar Dokokin Jihar Ondo Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar

Kotu Ta Hana Majalisar Dokokin Jihar Ondo Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar

  • Wata babbar kotun tarayya ta hana majalisar dokokin jihar Ondo daga shirin dakatar da mataimakin gwamnan jihar
  • Kotun mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta kuma hana gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, naɗa wani sabon mataimakin gwamnan
  • Alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite ya kuma ɗage sauraron ƙarar har ya zuwa ranar, 9 ga watan Oktoba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja -Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, ta hana majalisar dokokin jihar Ondo tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke bayan lauyan Aiyedatiwa, Kayode Adewusi, ya shigar da ƙarar, ya buƙaci umarnin ya fara aiki nan take, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Kotu ta hana majalisa tsige Lucky Aiyedatiwa
Kotu ta hana majalisa dokokin jihar Ondo daga tsige Lucky Aiyedatiwa Hoto: Luck Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Alƙalin ya kuma hana gwamna Rotimi Akeredolu naɗa sabon mataimakin gwamna tare da miƙa sunansa ga ƴan majalisar domin amincewa da shi, har sai lokacin da aka kammala sauraron ƙarar.

Mai shari’a Nwite ya ce bayan ya saurari Adewusi, yana da ra'ayin cewa adalci shi ne a amince da buƙatun mai shigar da ƙarar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Saboda haka, masu shigar da ƙara sun yi nasara kan ƙorafe-ƙorafensu." A cewarsa.

Meyasa Aiyedatiwa ya shigar da ƙarar?

Mataimakin gwamnan a cikin ƙarar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1294/2023, ya kai ƙarar Sufeto Janar na ƴan sanda da hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS).

Sauran sun haɗa da gwamna Akeredoku, shugaban majalisar dokoki, alƙalin alƙalan jihar Ondo da kuma majalisar dokokin jihar.

A cikin ƙarar waccce Mista Adelanke Akinrata ya shigar a ranar 21 ga watan Satumba, Aiyedatiwa ya nemi a biya masa buƙatu huɗu.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Majalisa Ta Aike da Saƙo Ga Mataimakin Gwamnan APC Kan Shirin Tsige Shi

Alkalin ya kuma bayar da umarnin dakatar da Akeredolu, hadimansa ko wasu daban daga cin zarafi, tsoratarwa da hana Aiyedatiwa gudanar da ayyukan ofishinsa na mataimakin gwamnan jihar Ondo.

Mai shari’a Nwite, wanda ya amince da dukkanin buƙatun da Aiyedatiwa ya nema, ya kuma ɗage ƙarar har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba domin cigbaba da sauraronta, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Majalisa Ta Musanta Batun Karbar Cin Hanci

A wani labarin na daban kuma, majalisar dokokin jihar Ondo ta musanta zargin cewa an ba kowane ɗan majalisa cin hancin N5m, domin tsige mataimakin gwamnan jihar.

Majalisar ta bayyana zargin a matsayin yunƙurin ɓata mata suna, inda ta ce tana da dalilinta na fara yunƙurin tsige Lucky Aiyedatiwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel