Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Fara Bin Matakan Tsige Mataimakin Gwamna

Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Fara Bin Matakan Tsige Mataimakin Gwamna

  • Majalisar dokokin jihar Ondo ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa daga kujerarsa
  • Rahotanni sun bayyana cewa majalisar ta kira zaman gaggawa ranar Laraba kuma tuni mambobi suka goyi bayan tsige shi
  • Wata majiya ta ce mataimakin gwamnan ya jefa kansa cikin rikici ne sakamakon abin da ya aikata lokacin da gwamna yake jinya a Jamus

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Alamu masu ƙarfi da ke fitowa ranar Laraba sun nuna cewa mambobin majalisar dokokin jihar Ondo sun fara ɗaukar matakan tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

Tribune Online ta tattaro cewa wannan na zuwa ne biyo bayan wani zaman gaggawa da majalisar dokokin ta kira yau Laraba, 20 ga watan Satumba, 2023.

Mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Fara Bin Matakan Tsige Mataimakin Gwamna Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

An tsaurara matakan tsaro a kewayen zauren majalisar da kuma babbar ƙofar shiga yayin zaman gaggawan da mambobin suka gudanar.

Kara karanta wannan

Rikici: Magana Ta Ƙare, Gwamnan PDP Ya Ƙori Mataimakin Gwamna Daga Gidan Gwamnati, Sanarwa Ta Fito

An tattaro cewa aƙalla yan majalisu 23 daga cikin mambobin majalisar jihar Ondo sun rattaɓa hannu tare da goyon bayan matakin tsige mataimakin gwamnan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me ya sa majalisa zata tsige mataimakin gwamnan?

Wata majiya ta ce yanzu haka ana binciken mataimakin gwamnan bisa zargin yin amfani da mukaminsa ba ta yadda ya dace ba kuma mai yiwuwa a raba shi da kujerarsa ta hanyar tsige shi.

A cewar majiyar, taƙaddamar ta fara ne a lokacin da Mista Aiyedatiwa ya amince da ware Naira miliyan 300 don siyan motar sulƙe kirar SUV domin amfanin kansa.

Majiyar ta ce ya fitar waɗan nan kuɗaɗen ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Ondo ke jinya a kasar Jamus kuma kuma ba tare da sanin gwamnan ba.

Ya ce Mataimakin Gwamnan ya kara dagula al’amura ne yayin da ya bayar da umarnin a fitar da kuɗin daga cikin asusun tallafin rage raɗaɗin cire tallafin mai na talakawa.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: An Kama a Wani Mutumi da Ake Zargi da Lalata da Ɗiyarsa, Ta Mutu a Yanayi Mai Mamaki

“Wannan asusun da gwamnatin tarayya ta samar, an yi shi ne don tallafa wa jihohi domin biyan bukatun mutanen jihohinsu," in ji majiyar.

Majiyar ta ce zaman tsigewar ya nuna aniyar Majalisar na tabbatar da sauke haƙkin talakawa, hatta a manyan matakan gwamnatin jihar.

Malamin Addini Ya Gargadi Atiku da Obi, Ya Ce Guguwar Sauya Sheka Na Nan Tafe Ga LP da PDP

A wani labarin kuma Malamin Coci ya yi hasashen manyan jiga-jigan da ka iya fice wa daga jam'iyyun adawa PDP da LP.

Saboda haka ya shawarci manyan jam'iyyun adawar guda biyu da su koma gida su sake shiri da dabaru kuma su tabbata sun yi abinda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262