Reno Omokri Ya Yi Hasashen Sakamakon Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Jihar Legas

Reno Omokri Ya Yi Hasashen Sakamakon Hukuncin Kotun Zaben Gwamnan Jihar Legas

  • Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya yi hasashe hukuncin kotun zaɓen gwamnan jihar Legas
  • Ƴan adawa dai na ƙalubalantar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar a ranar 18 ga Maris
  • Omokri ya fito fili ya yi watsi da fatan samun nasarar jam'iyyar Labour, inda ya haifar da martani iri-iri a manhajar X (wanda a baya aka fi sani da Twitter)

Ikeja, jihar Legas - Reno Omokri, wani fitaccen mai goyon bayan jam'iyyar PDP, ya yi hasashen sakamakon hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Legas.

Legit.ng ta rahoto cewa kotun zaɓen ta shirya yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar kan jam'iyyar APC mai mulki.

Reno Omokri ya bayyana wanda zai yi nasara a shari'ar zaben gwamnan Legas
Reno Omokri ya yi hasashen kotu za ta tabbatar da nasarar gwamna Sanwo-Olu Hoto: Reno Omokri, Gbadebo P Rhodes-Vivour, Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Omokri yayi hasashen rashin nasara ga Rhodes-Vivour

Kara karanta wannan

Yan Majalisa Sun Karbi Cin Hanci Domin Tsige Mataimakin Gwamnan APC? Gaskiya Ta Bayyana

Omokri ya rubuta a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Bata lokaci ne kawai zaman jira domin jin hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Legas."
"Babu wani abu da za a yi tsammani. Za a yi watsi da ƙalubalen sake zaben gwamna Sanwo-Olu saboda rashin cancanta, sannan aƙalla ɗaya daga cikin ɓangarorin (Gbadebo Rhodes-Vivor) ne zai ɗaukaka ƙara."
"Babu wani abun mamaki, GRV da Jandor sun sha kaye a hannun Sanwo-Olu cikin ruwan sanyi. Idan an yi sahihi, dole ne mu koyi amincewa da sakamakon zaɓenmu, ko kuma dole mu fuskanci shan kashi a hannun kotu."

Wane irin martani aka yi masa?

@OluwaEazy_ ya rubuta:

"Kamata ya yi a ce sun amince da sakamakon zaɓen, amma sai suka tafi kotun domin ƙaƙubalantarsa. A bayyane yake mun san cewa ba su da wani abun dogaro."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin Labour Party Da APC Kan Kujerar Dan Majalisa

@aslentoye ya rubuta:

"Sannu da ƙoƙari Mista INEC, Mista shari'a. Alƙalin komai."

@Adatwice ta rubuta:

"Ka gaya wa Atiku ya amince da kayen da ya sha, uh ashe yanzu Tinubu ka ke yi wa aiki."

@isujah_kennedy ya rubuta:

"A yayin da tabbas da gaske ne babu wani abin da za a yi tsammani, amma ba a isa a musanta cewa zaɓen ba a yi adalci ba. An tafka maguɗi da hana masu kaɗa ƙuri'a yin zaɓe."

APC Ta Yi Nasara Kan Labour Party a Kotu

A wani labarin kuma, jam'iyyar APC ta samu nasara kan jam'iyyar Labour Party, (LP) a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun jihar Legas.

Kotum zaɓen ta ƙwace kujerar ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Amuwo-Odofin II, Olukayode Doherty na jam'iyyar LP inda ta miƙa ta a hannun Rauf Olawale Sulaiman na Jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel